Labarin Dujjal da Annabi Isa (A,S) 6

🍂🍂🍂

LABARIN DUJJAL DA SAUKOWAR ANNABI ISAH (AS) (6)

Bayan haka ne sai Annabi Isah عليه الصلاة والسلام da sahabbansa su sauko kasa sai su ga babu masakar tsinke duk gawar Yajuj da Majuj da warinsu ya cika wajen, sai Annabi Isah عليه الصلاة والسلام da sahabbansa su roki Allah سبحانه وتعالى sai Allah سبحانه وتعالى ya aiko da wasu tsuntsaye kamar girman wuyan rakumi da ake kira "Al-Bukht" sai su dauki gawarwakin su watsar da su inda Allah سبحانه وتعالى ya so. Bayan nan sai Allah سبحانه وتعالى ya saukar da ruwan sama ya wanke duk wani gida da aka yi shi da laka ko gashi, sannan ya wanke kasa ita ma ta fita fes.

Za a umarci kasa ta fitar da ya'yan itacenta, ta kuma dawo da albarkatunta. A wannan lokacin jama'ar mutane za su ci ruman guda daya su koshi su kuma zauna karkashin inuwar ganyensa. Za a sanya albarka a cikin madararsu ta yadda madarar rakuma daya zata isa wata kungiyar mutane. Madarar saniya kuma zata isa wata kabila guda. Madarar akuya kuwa zata isa wani dangi.

Kasa zata cika da aminci, zakuna za su yi kiwo tare da rakuma, damisa tare da shanu, kura tare da tumaki. Yara za su yi wasa da maciji amma ba zai cuce su ba. A lokacin ba a bauta wa komai sai Allah سبحانه وتعالى.

Annabi Isah عليه الصلاة والسلام zai zauna a ban kasa shekara ar'bain, sai Allah سبحانه وتعالى ya dauki ransa sai musulmi su yi masa Sallah صلوات الله وسلامه عليه.

MATAKAN KARIYA DAGA FITINAR DUJJAL

🔸 Mutum ya yawaita neman tsarin Allah سبحانه وتعالى daga sharrin fitinar Dujjal musamman a zaman tahiya ta karshe cikin sallar farilla da ta nafila. Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Idan dayanku ya gama tahiya ta karshe ya nemi tsari daga abubuwa guda hudu: Azabar jahannama da azabar kabari da fitinar rayuwa da mutuwa da kuma fitinar Dujjal".

🔸 Haddace ayoyi goma na farkon Suratul Kahfi. Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Duk wanda ya haddace ayoyi goma na farkon Suratul Kahfi za a kare shi daga fitinar Dujjal".

A karshe, imani da aiki na gari shi ne babban dalilin samun tsira daga fitinar Dujjal

               الله تعالى اعلم

✍🏻 Umm Khaleel

                           🍂🍂🍂