Labarin Dujjal da Annabi Isa (A,S) 5

🍁🍁🍁

LABARIN DUJJAL DA SAUKOWAR ANNABI ISAH (AS) (5)

Annabi Isah عليه السلام zai zama shugaba mai hukunci da adalci, zai jagoranci mutane da Alqur'ani da sunnar Annabi صلى الله عليه وسلم. Zai karya salib (cross), zai yanka alade, zai dakatar da yaki, kudi zai kwarara har ya zama babu mutum daya da zai karba, sujjada guda daya ta fi duniya da abin da yake cikinta, zai jire jizya .....

Annabi Isah عليه الصلاة والسلام zai zo wajen wasu mutane wadanda Allah سبحانه وتعالى ya kare su daga Dujjal sai ya shafe kura daga fuskokinsu ya kuma ba su labarin matsayinsu a Aljanna. Yana cikin haka ne sai Allah سبحانه وتعالى ya yi wahayi zuwa gare shi cewa: "Hakika Ni na fitar da wasu bayina wadanda babu wani wanda zai iya yakarsu saboda haka ka ajiye wadannan bayi nawa a 'Tur Sinà'", (dutsen da Allah سبحانه وتعالى ya yi magana da Annabi Musa عليه الصلاة والسلام).

Allah سبحانه وتعالى zai fito da Yajuj da Majuj, sai su fito suna tafiya da sauri su watsu. Kungiya ta farko daga cikinsu zasu wuce ta wajen wani tafki da ake kira "Tabariyah" sai su shanye duk ruwan cikinsa. Idan kungiya ta bayansu suka zo wuce wa ta wajen sai su ce lallai da kuwa akwai ruwa a wajen nan.

Annabi Isah عليه الصلاة والسلام tare da sahabbansa an kewayesu can a kan dutse har ya kasance kan  Sa a wajen dayansu ya fi dinare dari a wajen daya daga cikinku a yanzu. Sai Annabi Isah عليه الصلاة والسلام da sahabbansa su yi addu'a su roki Allah سبحانه وتعالى sai Allah سبحانه وتعالى ya turo wa Yajuj da Majuj wata tsutsa wacce ake kira 'Annagaf' a wuyansu sai kawai a wayi gari ta karya musu wuya duk sun mutu.

Bayan haka ne sai Annabi Isah عليه السلام da sahabbansa su sauko kasa sai su ga babu masakar tsinke duk gawar Yajuj da Majuj da warinsu ya cika wajen ....

                     الله تعالى اعلم

✍🏻 Umm Khaleel

                       🍁🍁🍁