Kyauta gyara sashe

Ma’anar Kyauta: Na nufin wani aiki ne wanda mutum kan yi ta hanyar bayarwa , ko mika wani abin hannunsa (kudi ko tufafi ko abinci ko dabba, ko wani abu) zuwa ga wani. Ta hanyar mikawa hannu da hannu, ko kuma ta hanyar aikawa da dan aike.

Akan kira mai yin kyauta namiji da karimi, mace kuma ma’abuciyar kyauta, idan jam’i ne kuma a kirasu masu karamci.

Dabi'a: Na nufin hali wanda aka san mutum da shi wanda yake aikatawa yau da kullum ya zamar masa jiki.

Baiwa: Na nufin wata ni’ima wadda Allah Ya yi wa mutum. Wannan ni’imar kuma mai ita kan yi amfani da ita a kowane lokaci, ta ko wacce fuska idan wani al’amari ya taso ya taimaka wa waninsa don samun mafita.

Wauta: Na nufin raunin hankali wanda mai shi yakan yi amfani da shi. A wani lokaci akan kira wauta da hauka.

KYAUTA A MAHANGAR AL’ADAR BAHAUSHE gyara sashe

Kyauta a mahangar al’ada, ana iya cewa wata dabi’a ce muhimmiya. Wannan yasa gaba daya al’adar Bahaushe take kaunar kyauta da kuma mai kyauta(karimi).

Tabbas mutum mai kyauta na da farin jini da kwarjini da mutunci a cikin al’ummar Hausawa. Matukar aka san mutum maikyauta ne, a wani lokaci har kokarin auren yayansa ake yi, ko kuma idan shi ya nema a ba shi. A mafi yawan lokutta, kowa kan so yin ma’ammala da shi.

Al’adar Bahaushe ta camfa auren maikyauta, shi yasa ake kwadayin aurensa ko kuma a auri yarsa, don fatan a haifi da ya gado shi wajen kyauta. Bisa dalilin cewa kyauta na cikin dabi’u da akan gada daga uwa. Haka nan kuma akan iya koyon dabi’ar kyauta daga abokin zama ko makwabci. Bahaushe ya ce: “zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai".

Bisa wannan dalilai ne yasa Bahaushe ya dauki kyauta a matsayin dabi’a.  Kyauta dai ita ce ka bai wa wani mutum alheri ko hasafi na kudi, tufafi, abinci ko dabba, kai da dai sauransu. Kyauta kan yara kulla zumunci ta inda zaka samu da ya  yi wa iyayensa, ko yaya ya yi wa kannin sa, ko aboki ya yi wa abokinsa, ko makwabci da maƙwabci, duk kuwa inda kyauta ta ratsa ko ta gitta, to lallai zaka samu ƙauna a tsakani. Akwai wasu kalmomi da akan faɗa in za a yi kyauta, kamar  ungo ko amshi ko karbi ko debi ko dauki ko bar shi da sauransu.

Bahaushe ya dauki kyauta da muhimmanci, don kuwa Bahaushe ya dauketa kamar wata igiya ce da ke kulla zumunci ko kuma kara wa babba girma, da kauna da kwar jini ga sauran jama’a.

Kyauta kan kara wa babba girma don kuwa har Karin Magana Bahaushe ya yi game da kyauta: “Laifin yaro }kyuwuya laifin babba rowa” ko “Yaba kyauta tukwici” da dai makamantansu, misalin inda kyauta ke kara wa mutum girma, shi ne inda sarki ko shugaba zai bai wa talakansa ko wani mutum na kasa da shi kyauta, ko miji ya yi wa matarsa kyauta.

Akwai inda kyauta kan zama don tausayawa a inda zaka ga mutum na cikin matsayi na bukatar taimako, amma fa ya sha bamban da sadaka. Bayan wannan kuma, sai inda kyauta kan zama abin neman fada, kamar dai cin hanci ko toshiyar baki ko kuma rashawa. Ko da yake akan yi mata lullubi a ce mata na goro, a nan kuwa ta kan taso ne a inda wani mutum yake neman wani abu a wurin wani mutum mai mukami ko kuma yana da shari’a ko dai makamantansu.

IRE-IREN KYAUTUTTUKA. DALILIN YIN SU. gyara sashe

1- Hasafi - Don ciwo ko haka kurum.

2- Toshi - Don samartaka ko zawarci.

3- Barka da Sallah - Don bikin Sallah, Ranar Sallah.

4- Cin hanci. - Don neman wata alfarma.

5- Maula - Don neman girma.

6- Tukwici - Don nuna godiyar wata kyauta.

7- La’ada - Don shaidar ciniki.

8- Shara - Don cikar shekara tsakanin abokan wasa.

9- Gudunmuwa - Taimako don wani sha’ani.

10- Gyara - Don sayayya (Ciniki).

11- Tsaraba - Don tafiya.

12- Gara - Don aure.

13- kantiya - Don haihuwa.

14- Ka-fi-mai- kora – Don kishiya.

15- Dannar kirji – Don kishiya

16- Kayan fadar kishiya – Don kishiya 17- Taimako domin gajiyayye

MUTANEN DA KYAUTUTTUKAN KAN SHAFE SU. gyara sashe

1- Hasafi - Aboki ko dan’uwa ko Makwabci.

2- Toshi - Masoya ko Budurwa ko Saurayi ko Bazawara.

3- Barka da Sallah - dan’uwa ko Yara ko 6ammata.

4- Cin hanci. - Shugaba ko Mai Mulki ko Talakawa.

5- Maula - Maroka ko kanraraka ko Masu kudi.

6- Tukwici - Manya da Yara.

7- La’ada - ‘dan kasuwa, sauran jama’a.

8- Shara - Abokan wasa ko dan’uwa.

9- Gudunmuwa - dan’uwa ko Abokai ko Mata ko Maza.

10- Gyara - Ma’auna, Masu kayan miya da sauransu.

11- Tsaraba - Baƙo da mai masauki.

12- Gara - Iyaye kan yi wa yarsu in an yi mata aure.

13- kantiya - Miji kan yi wa matarsa a haihuwar farko.

14- Ka-fi-mai- kora - Iyaye kan yi wa yarsu in za a yi mata kishiya.

15- Dannar kirji – Dangi kan yi wa mace in za a yi mata kishiya.

16- Kayan fa]ar kishiya – Miji kan yi wa matarsa in za a yi mata kishiya.

Ga wasu dabaru na yin kyauta cikin hikima guda bakwai wadanda Bahaushe ya gado, tun iyaye da kakanni, ko da yake a yau masu aikatasu sun yi karanci matuka. Wadannan dabi’u kuwa, su ne: -

1- Ciyayya.

2- Kawo kwarya.

3- Marka-marka.

4- Dauki.

5- Ziyara.

6- Gudummuwa.

7- Aikin gayya.