Kwararrafa, wata tsohuwar daula ce da rukunin ƙabilun da ake kira Ƙawancen-Kwa (Kwa-Group) suka kafa ta a yankin Arewacin Kogin Binuwai.

Kalandan na kwararrafa
wakar shehu shagari wace akayi maganar kwararfa

Daula ce da wasu masana tarihi suke ganin an kafa ta a cikin ƙarni na 14. Ta kuma yi sharafinta daga wannan ƙarni har zuwa cikin ƙarni na 17 (Dinslage da Leger, 1996). Haka nan, Okpeh da Ochefu (babu lokacin bugu) sun ambata cewa tarihi ya tabbatar da samuwar wata daula mai suna Kwararrafa a arewa da kogin Binuwai. Wannan daula ta haɗaka tsakanin waɗannan ƙabilu masu asali guda, Jukunawa ne suka shugabance ta.[1]

Asali da Yararruka

gyara sashe

Rubuce-rubuce masu tarin yawa, kamar irin su Dr. Dawuda (2011), Mac-Leva (2009), Okunna, Emman, Gausa, da Solomon, (2014), Ujorha (2012), Dinslage da Leger (1996), sun ruwaito cewa, yarurrukan da suka kafa wannan daular ƙwance ta Kwararrafa daga Gabas suka fito tare da ayyana Yamen a matsayin tushen su.[2]

Yarurruka Yarurrukan da suka haɗu suka kafa wannan daula ta haɗaka suna da tarin yawa, amma kaɗan daga cikin su sun Onawo da: Jukun, Igala, Ibira , Idoma, Alago (Boumo, 2011; Onawo, 2016), Boumo (2011) ya ƙara da Nupe, Mada, Kantana, Rindre, Eggon, Bassa Nge da Bassa Komo. Onawo (2016), ya ƙara da Goemi, Migili, Etulu, Iyala da Aros. Dinslage da Leger (1996), kuma suka zayyano Kwami, Kupto, Kushi, Piya, Bole, Bantu, Bole, Ngamo, Karekare, Kirfi, da Galembi. Andoma na Doma; wato Onawo(2016), ya ce, Jukunawa su ne shugabanni tare da Aku a matsayin jagoran addini.[3]


Yaƙuƙuwa

gyara sashe

Mutanen Daular Kwararafa, mutane ne masu matuƙar jarumtaka wajen yaƙi, an ruwaito cewa, sun yi galaba a yaƙin da suka gwambza da manyan masarautun ƙasar Hausa waɗanda suka haɗa da Kano , Katsina , Dutse , Ningi, da kuma Zazzau (Wikipedia, 2016; Northern Nigerian Publishing Company, 1970; Sanusi, 2009). Wannan magana, ana iya ƙarfafarta da sunayen wasu unguwanni guda biyu da ke cikin garuruwan Kano da Zariya. Agarin Kano akwai wata unguwa mai suna “Yakasai”, wacce ruwayar kunne-ya-girmi-kaka ta sheda mana cewa kalma ce da ke nufin “Za mu dawo ko muna dawowa” wacce ta fito daga bakin su Jukunawa a lokacin da suka ci Kano da yaƙi. Haka nan kuma akwai unguwa mai suna ‘Tudun Jukun” a cikin garin Zariya.[4]

Durƙushewa Rikicin shugabanci (tattaunawa da sarkin Pindiga), gujewa hare-hare daga daular Barno ta wani gefen, da kuma mayaƙan musulunci na daular Shehu Ɗanfodiye daga wani gefen (David, 2013; Boumo, 2011), na daga cikin manyan dalilan da ya kawo ƙauracewar wasu yarurrukan daga wannan yankin suka ƙetara zuwa kudu da Kogin na Binuwai.[5]


Manazarta

gyara sashe
  1. http://ebirayouthforumassociation.blogspot.com.ng /2013/05/history-of-ebira-people.html
  2. http://www.dailytrust.com.ng/weekly/index.php/feature s/10585-did-the-jukun-originate-from-egypt
  3. Boumo E. (2011). Factoring Inter-Group Relations In The Lower Benue Valley To Circa 1900 A.D. Department of History, Benue State University Makurdi, Benue State, Nigeria. African Journal of Arts and Cultural Studies Volume 4, Number 2, 2011
  4. Sanusi N. M. (2009). Stories of Dutse Palace 1421 – 2009. An buga wannan littafi a maɗaba’ar jahar Jigawa.
  5. http://www.nobleworld.biz/images/Edo.pdf