Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Bauchi

Kwalejin Kimiyya a Najeriya

Kwaalejin Kimiyya da Fasaha, Bauchi[1] ɗaya daga manyan makarantu ne dake garin Bauchi, wanda ya kasance gari na hedikwatar masarautar gargajiya kana kuma babban birnin jihar Bauchi, dake Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Bauchi
Bayanai
Suna a hukumance
Federal Polytechnic, Bauchi
Iri polytechnic (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Harshen amfani Turanci
Tarihi
Ƙirƙira 1979
fptb.edu.ng
Daliban Makarantar Folitakanic ta Bauchi

An kafa Kwalejin Fasaha ta Tarayya ta Bauchi a watan Yulin shekarata 1979, ta hanyar Dokar 33, (Decree 33). na Tarayyar Najeriya tare da wasu cibiyoyin har guda shida tare da izinin gudanar da karatu na cikakken lokaci da / ko kuma rabin lokaci akan darussan fannoni na Fasaha, Ilimin Kimiyya, Kasuwanci, Gudanarwa da sauran wasu fannonin da suka dace don buƙatar ci gaban Nijeriya. Tana nan a ƙauyen Gwallameji, hanyar Bauchi - Dass. Shugaban makarantar na yanzu shi ne Arch. Sanusi Waziri Gumau. Tsangayoyin da ke bayar da karatun da za su kai ga kyautar difloma ta kasa da babbar difloma na makarantar sun samu amincewa don gudanar da kwasa-kwasan digiri tara a shekarar 2020, da hadin gwiwar Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi.

A makarantar a na koyar da waɗannan kwasa-kwasan;

 • Accountancy.
 • Agricultural and Environmental Engineering Technology
 • Agricultural Technology.
 • Animal Health and Production Technology.
 • Architectural Technology.
 • Banking and Finance.
 • Building Technology.
 • Business Administration and Management.
 • Chemical Engineering Technology.
 • Computer Science.
 • Electrical/Electronic Engineering.
 • Estate Management and Valuation.
 • Food Technology.
 • Hospitality Management.
 • Leisure and Tourism Management.
 • Mass Communication.
 • Mechanical Engineering Technology.
 • Office Technology and Management.
 • Public Administration.
 • Quantity Surveying.
 • Science Laboratory Technology.
 • Statistics.
 • Surveying and Geo-informatics.

Manazarta.

gyara sashe
 1. https://www.google.com/amp/s/punchng.com/protesting-bauchi-students-barricade-road-over-robbery-attacks/%3famp