Kwalejin Horar da Jirgin Sama na Emirates

Makarantar koyan jirgin sama da ke Dubai

Emirates Flight Training Academy ( EFTA ; Larabci: أكاديمية الإمارات لتدريب الطيّارين‎ ), makarantar horar da matukan jirgi ce da ke cikin Hadaddiyar Daular Larabawa. An kafa ta a shekarar 2017, wani reshe ne na kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa da ƙasa, The Emirates Group, da sashin jirgin sama, Emirates.[1][2]

Kwalejin Horar da Jirgin Sama na Emirates
Bayanai
Iri makaranta
Ƙasa Taraiyar larabawa
Tarihi
Ƙirƙira 2017
emiratesflighttrainingacademy.com…

An bude makarantar a hukumance a shekara ta 2017 a lokacin Dubai Airshow kuma an fara amfani da tarin jiragen sama na horo shida.[3] Shirye-shiryen sun haɗa da jimillar jirage 27: 22 Cirrus SR22s da ƙwara biyar na Embraer Phenom 100s. [4]

Tare da nasa filin jirgin sama mai zaman kansa da harabar makarantar, makarantar tana a gefen filin jirgin saman Dubai World Central Airport, kuma za ta yi aiki a matsayin cibiyar horarwa don Shirin Pilot na ƙasa da kuma ɗalibai na duniya.[5] A cikin 2017, makarantar ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da kamfanin ƙera jiragen sama na Amurka Boeing don haɗin gwiwa kan tsarin horo don sarrafa koyo da horar da ayyukan jirgin sama. [5]

Duba kuma

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. Staff (13 November 2017). "Emirates Flight Training Academy inaugurated at Dubai Airshow". The Journal For Civil Aviation Training. Archived from the original on 23 June 2018. Retrieved 27 April 2018.
  2. "AFTA-About". Arab Flight Training Academy. Retrieved 27 April 2018.
  3. "Emirates Flight Training Academy inaugurated at Dubai Airshow". The National (UAE). 13 November 2017. Retrieved 5 May 2018.
  4. Emirates Flight Training Academy receives delivery of first training aircraft
  5. 5.0 5.1 John Morris (11 November 2017). "Emirates Flight Training Academy Opens". Aviation Week. Retrieved 5 May 2018.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe