Kwaikwai wanda aka fi sani da Hyperemesis gravidarum (HG), yanayi ne da mace me ciki ke kamuwa dashi a farkon samun ciki wanda ya hada da yawan jin tashin zuciya, zazzabi, rage nauyin jiki, amai, yawan bacci, rashin cin abinci da kuma yawan suma.Ana iya daukan shi a mafi tsananin zazzabin safe. Sau da yawa alamun suna kai tsawon mako na 20 na ciki amma za su iya ci gaba har tsawon watannin ciki zuwa haihuwa.