Kunshi wanda aka fi sani da lalle. Mata a cikin al'ummar Hausawa su aka sani da yin kumshi wato lalle wanda har shari`ar musulunci ta halatta masu yin kumshi saboda kariya ne ga lafiyar su. Kuma ana yi ne domin ado ko kwalliya. Lalle yana da matukar amfani ga lafiyarsu saboda idan mace ta yi kumshi yana bin duk wata jijiyar jininta tun daga tafin kafarta har zuwa kwakwalwa. Lalle yana kariya daga kamuwa da cutar sanyi na mata wanda aka fi sani da [infection] sannan kuma yana daidaita wa mace al'adarta. Musamman wadda take yi mata wasa ko kuma takan dauki lokaci ba ta yi ba, kamar misalin masu yi sau daya a shekara ko masu yin wata biyu ko uku ba su yi ba. Irin wadannan matan idan har za su lizunci yin lalle a kodayaushe to insha Allah lalle zai magance masu wannan matsalar. Lalle ya kasu kashi biyu, akwai lallen gargajiya shi ne wanda muke magana akanshi akwai kuma [dyes] wanda aka fi sani da lallen daba na gargajiya ba, amma dukkansu ana yinsu don kwalliya ko ado na gargajiya. Irin wannan kumshin shi ne wanda musulunci ya halatta a yi.

Manazarta

gyara sashe

[1]

  1. https://www.babycenter.in/babyname/1075243/kunshi