Kungiyar Shari'a ta Gabashin Afirka

Kungiyar gabashin Afrika ta Lauyoyi

Ƙungiyar Lauyoyin Gabashin Afirka (EALS) ita ce haɗa-kar Ƙungiyar Lauyoyin yankin Gabashin Afirka. An kafa ƙungiyar a shekarar 1995 kuma hedkwatar kungiyar na a ƙasar Tanzaniya. EALS na da mambobi sama da 42,000, kuma tana da ƙungiyoyin lauyoyi bakwai na ƙasa a matsayin mambobi: Law Society of Kenya, [1] Tanganyika Law Society, [2] Uganda Law Society, [3] Zanzibar Law Society, Rwanda Bar Association, [4] Ƙungiyar Lauyoyin Burundi, [5] Ƙungiyar Lauyoyin Sudan ta Kudu da Ƙungiyar Ƙwararrun Ƙwararru ta ƙasar Habasha. Ƙungiyar Ƙwararrun Ƙwararru ta lauyoyi a Habashe ce ƙungiyar baya-baya nan da ta shiga Ƙungiyar.

Kungiyar Shari'a ta Gabashin Afirka
Bayanai
Iri ma'aikata
Mulki
Hedkwata Arusha (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 1995
ealawsociety.org

Ƙungiyar Lauyoyin Gabashin Afirka na aiki don inganta kyakkyawan shugabanci da bin doka a yankin Gabashin Afirka kuma tana sa ido tare da al'ummar Gabashin Afirka [6] da Hukumar Haƙƙin Dan Adam da Jama'ar Afirka. EALS kuma memba ce ga Ƙungiyar Ƙasa ta Duniya don Haƙƙin Kare [7] wanda shugabannin kowace ƙasa suka yi alƙawarin kare mutanensu daga kisan kiyashi, laifuffukan yaki, kawar da ƙabilanci, dama laifuffukan cin zarafin bil Adama.

Taron Babban sashin yanke shawara na haɗa-kar ƙungiyar EALS shine babban taronsu na shekara-shekara [3] wanda kwararrun masana shari'a ke haɗuwa don duba ci gaban da aka samu na shekarar da ta gabata da kuma tsara hanyar ci gaba na shekara mai zuwa a gaba.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Welcome to LSK". lsk.or.ke. Retrieved 2022-04-22.
  2. "Tanganyika Law Society - Law Association". tls.or.tz.
  3. "Home | Uganda Law Society". www.uls.or.ug. Retrieved 2022-04-22.
  4. [1][dead link]
  5. [2] [dead link]
  6. "EAC Institutions".
  7. "ICRtoP participates in Eastern Africa Civil Society Forum (EACSOF), RtoP included in final communiqué". Archived from the original on 11 January 2019. Retrieved 11 January 2019.

Hanyoyin hadi na Waje

gyara sashe