Kolopopo ƙauye ne a Wallis da Futuna, wanda shine tarin tsibiri na Faransa a Kudancin Pacific mai ɗauke da ƙauyuka 36.Tana cikin gundumar Mua a kudu maso yammacin gabar tekun Wallis.Yawanta bisa ga ƙidayar 2018 mutane 99 ne. Yawan jama'a ya ragu a wannan yanki saboda rashin aikin yi da kuma rikicin siyasa a babban tsibirin.Kudin da ake amfani da shi shine Comptoirs Français du Pacifique (CFP) Franc.

Babban ƙabila a wannan yanki na tsibiri ita ce Polynesia.Kusan kashi 60% na yawan jama'a suna magana da Wallisian,28% suna jin Futunan kuma sama da kashi 12% suna jin Faransanci.Kashi 99% na mazauna wannan yanki mabiya addinin Roman Katolika ne.