Kogin Lilongwe kogi ne a Malawi;yana bi ta Lilongwe,babban birnin kasar.

Kogin ya kai kusan 200 km tsayi.Yana kwarara zuwa tafkin Malawi.

Ya samo asali ne daga gandun dajin Dzalanyama a kan iyakar tsakanin gundumomin Lilongwe da Dedza.

Kogin Lilongwe shine babban tushen ruwa ga mazauna birnin Lilongwe.