Kofar Soro Wata Unguwa ce dake cikin garin Katsina, Unguwar tana gaba da Folis Siteshin ta tsakiya wato (Central Police Station). Unguwar tayi matukar suna saboda dalilai da dama da suka hada da zamanta wajen zama ga uba kuma Sarki na Mutanen Garin Katsina wato Alh. Dr. Abdulmuminu Kabir Usman.