Kofar Sauri tana da matukar tarihi, Kofar tana gabas maso arewa da birnin Katsina, kofar ta yi iyaka ne da Unguwar Rafukka, Nasarawa, Makera da kuma Yammawa.

Kofar Soro
Kofar Sauri

Tarihin kofar sauri

gyara sashe

Bayanin kofar Sauri din, da kuma unguwannin da ke kusa da ita, Tarihi ya nuna cewa akwai bayanai guda biyu game da asalin wannan kofa ta sauri, a wani bayanin, an ce; kofar ta samo asali ne daga Shugaban samari na wannan lokaci, wanda ake kira da Sarkin samari, kuma ya zauna ne a daidai kofar ta Sauri, a kwana a tashi yau da gobe ta sanya aka fara takaita kalmar ‘Samari’ zuwa ‘Samri’, daga nan kuma ta koma ‘Sauri’ inda a karshe kuma ta koma kofar Sauri tarihi ya nunacewa daga nan ne aka samo kofar sauri.

A wani tarihin kuma an nuna cewa, a lokacin mulkin Ummarun Dallaje ne (1807-1835) wani mayaki da ake kira da Danbaskore, ya kawo wa Katsina hari ta wannan bangare amma sai ya iske duk kofofin garin a kulle a wannan lokacin, tarihi ya nuna cewa Sarkin Sauri, wanda wani gari ne da ke can wajen Kaita a yanzu, ya kawo ma Katsina gudunmawa ya fatattaki Danbaskore da mayakansa, bayan ya kori maharan, sai yayi sauri ya sa aka fasa kofa ta cikin ganuwar a inda ya kutsa kai, ya shiga birnin, ya shaida wa Sarkin Katsina na wannan lokacin duk abin da ya faru. Jin dadin wanan aiki da Sauri ya yi, ya sa aka sanya wa wannan kofa sunansa, ma’ana kofar Sauri.

Manazarta

gyara sashe