Ƙofar Durɓi
Kofar Durbi,kofa ce mai matukar tarihi, ada tarihi ya nuna cewar an sanya ma wannan kofa sunan Durbi ne saboda wani Hakimi na Habe, mai suna Durbi, wanda shi ne Hakimin garin Mani tun wajen karni na 15.
Kofar Durbi |
---|
Ta wannan kofar,ce yake fita zuwa Mani, ta nan ne kuma yake dawowa.
Daga shi wannan Hakimi ne na Mani ne aka rika kiran shi da Durbi.
A wani bayanin kuma, an nuna cewa, wannan kofa mai suna Kofar Durbi, ta samo sunanta daga sarautar Durbi-Ta-kusheyi. To daga nan ne, sunan Durbi ya fara a mulkin Katsina gaba daya, wanda kuma, ko da su Durbawar suka yi kaura, suka koma birnin Katsina, aka bar sarautar Durbi din da sunanta na asali, wato maimakon Durbi sai ta zama Durbin Katsina. A yanzu duk wanda ke rike da sarautar Durbi, shi ne kuma Hakimin Mani.
Ta ita wannan kofar yake shiga in ya dawo.Kofar Durbi ta yi makwabtaka da unguwannin da ke cikin ta, kamar unguwar Filin Samji da Sauransu.