Kimiyyar Tattalin Arziki

Kimiyyar Tattalin Arziki ko kuma Ilimin Tattalin Arziki shine ilimin zamantakewar al'umma wanda ke nazarin yadda mutane ke hulɗa da darajar abubuwa; musamman, samarwa (production), rarrabawa, da yin amfani da kayayyaki da kuma ayyuka (koko Sabis).[1] Daga turancin ingilishi ana kiran wannan ilimin "Economics" ana karantawa "ikonomis". Saboda samun saukin rubutu da na koyarwa, masu ilimin adabin hausa suna iya daukar matsaya guda domin a rinka kiran wannan kimiyyar "Ikonomis". Ganin cewar akwai banbanci tsakanin "Economy - Tattalin Arziki" da kuma "Economics - Kimiyyar Tattalin Arziki" za a iya cigaba da kiran tattalin arziki a matsayin halin arzikin kasashe da na mutane. Ikonomis kuma a cigaba da anfani da ita a mtsayin ilimin tattalin arziki. Tattalin arziki (ikonomis) yana mai da hankali ne kan halaye da mu'amala da jami'ai ko da wakilan hada-hada, da kuma yadda shi tattalin arzikin (Economy) ya ke aiki. Ilimin tattalin arziki ana iyi raba shi a sassa guda biyu. Sashi da kuma farko shi ke nazarin abubuwan asali a cikin tattalin arziki, gami da wakilai ɗai-ɗai da kasuwanni, hulɗarsu, da kuma sakamakon hulɗar tasu. Wannan sashe ana kiran shi a turanci "Microeconomics" a hausance za mu iya kiransa Tattalin Arziki ɗai-ɗai ko kuma Mikro Ikonomis. Sashe na biyu shi kuma yana nazarin tattalin arziki azaman shi na tsari inda ya ke nazarin manyan ƙididdigar tattalin arziƙi (tanadi, saka hannun jari, anfani, bunƙasar tattalin arziƙi). A turanci ana kiran wannan sashe "Macroeconomics", amma a husance za mu iya kiran wannan ilimin, "Tattalin Arziki Jimla" ko kuma (ikonomis).[2]

Samfurin Samarwa da Bukata

ManazartaGyara

  1. Economics Archived 2017-02-15 at the Wayback MachineOxford Living Dictionaries. Oxford University Press.
  2. Krugman, Paul; Wells, Robin (2012). Economics (3rd ed.). Worth Publishers. p. 2. ISBN 978-1-4641-2873-8.