Khadija Yobe
Khadija Yobe
Jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud, an fara sanin ta ne a fim Mai suna Izzar so , inda ta fito a suna karima.ta daukaka ne a sanadiyyar fim din Izzar so, daga Nan tayi bugun zuciyan masoya da sauran su.
Takaitaccen Tarihin ta
gyara sashe[1]Khadija Yobe Cikakken sunan ta shine Khadija shehu ko Khadija alhaji shehu, sunan da ake mata inkiya dashi shine karima Izzar so, ta samo sunan ne a fim din daya haskaka ta Mai suna Izzar so,an haifeta a shekarar 1995 a garin Maiduguri,Amma asalin iyayenta mutanen damaturu ne a jihar Yobe,tayi karatun firamare a garin Maiduguri, daga tai karatun sakandiri a damaturu,daga Nan ta shiga federal polytechnic damaturu inda ta Karanci kwas din public administration,ta Sami matakin karatu HND,ta fara harkan fim ne a shekarar 2018 ta fara da fim Mai suna wutar Kara, ta shiga fim sanadiyyar hijra dasu kayo a saboda Yan Boko Haram .jarumar tayi aure a shekarar 2023.