Karl Olutokun Toriola shugaban kasuwanci ne na Najeriya. Shine Babban Jami'in Kamfanin na MTN Nigeria.[1][2]

Karl Toriola
Rayuwa
Sana'a
Sana'a business executive (en) Fassara

Toriola ya yi Digiri na farko a fannin Kimiyyar Lantarki da Wutar Lantarki daga Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, Najeriya sannan ya yi Digiri na biyu a fannin Kimiyyar Sadarwa daga Jami’ar Wales, Swansea, Birtaniya.[3]

Ya yi aiki a Ericsson Nigeria a 2000 a matsayin Manajan Tallafi da Haɗin kai sannan ya koma Econet Nigeria a 2003 a matsayin mataimakin babban jami'in fasaha ya tashi ya zama babban jami'in gudanarwa a lokacin Vmobile Nigeria (yanzu Airtel).[4][5] A shekara ta 2006 Toriola ya koma MTN Nigeria a matsayin babban jami'in fasaha, Shugaba MTN Kamaru a wannan shekarar. Ya ci gaba da zama mataimakin shugaban WECA na MTN Group (West and Central Africa) na tsawon shekaru 5 har sai da aka sanar da shi shugaban kamfanin na MTN Nigeria a watan Oktoba 2020.[6]

Shi mamba ne na kungiyar Injiniya ta Najeriya, memba a Majalisar Dokokin Injiniya a Najeriya. da Cibiyar Gudanarwa. Yana kan Majalisar Mulki ta 12 a Jami’ar Jihar Legas, Nijeriya.[7][8]

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Karl yana da aure kuma yana da ɗa daya tilo, Damilola Karla Toriola.[9]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://en.wikipedia.org/wiki/Karl_Toriola#cite_note-1
  2. https://en.wikipedia.org/wiki/Karl_Toriola#cite_note-2
  3. https://en.wikipedia.org/wiki/Karl_Toriola#cite_note-3
  4. https://en.wikipedia.org/wiki/Karl_Toriola#cite_note-4
  5. https://en.wikipedia.org/wiki/Karl_Toriola#cite_note-5
  6. https://en.wikipedia.org/wiki/Karl_Toriola#cite_note-6
  7. https://en.wikipedia.org/wiki/Karl_Toriola#cite_note-7
  8. https://en.wikipedia.org/wiki/Karl_Toriola#cite_note-8
  9. https://en.wikipedia.org/wiki/Karl_Toriola#cite_note-9