Open main menu

Wikipedia β

Karin Magana

Duniya ta fi bagaruwa iya jima!

Wannan karin magana ne kuma habaici ne, Ana iya amfani da shi ga irin mutanen nan masu taurin kai wadanda ba su san abin da duniya ke ciki ba, to, idan aka kwabe su a kan wani lamari suka ki bi, a iya ce musu "Duniya ce, ta fi bagaruwa iya jima." Ma'ana ko abun nufi, wanda bai ji bari ba ya ji hoho.


k/magana takaitaccen lafazi ne na karin magana ko ko azanci Daga kin gaskiya sai bata

ana fadin wannan k/magana yayin da mutun ya san gaskiya, kuma ya danne ya yi kamar bai sani ba

3: Kome tsawon dare, gari zai waye. Ana fadin wannan k/magana ce, yayin da mutum ya shiga cikin kuncin rayuwa, kuma ya damu da yawa, kamar wani salo ne na hankurtarwa watakila ya zo ne daga ayar da ke cewa: tare da ko wani kunci akwai yalwa

4: Hangen DALA ba shiga Birni ba. Ana fadin wannan k/magana ce yayin da mutum ya dage don ya kai kansa gaba da matsayinsa na gaskiya, misali kamar mutumin da ya karanci wani bangare na littafin Fikihu a Mazhaba daya, sai ya fara kiran kansa shehun Musulunci'

5: ALBARKACIN KAZA 'KADANGARE YAKE SHAN RUWAN KASKO

Ana fadin wannan Karin Magana ce a yayin da wani mutum ya sami wani abu ko wani matsayi ta hanyar wani mutum. Misali ABDULLAHI YA SAMU AIKI A KAMFANIN TALIYAR DANGOTE NE, TA HANYAR ABOKINSA IBRAHIM. A nan sai Bahaushe ya ce ai dama ALBARKACIN KAZA NE KADANGARE KAN SHA RUWAN KASKO. Ma'anar wancan misalin na sama kenan a cikin KARIN MAGANA.

6: Munafunci dodo ne ya kanci mai shi. wannan karin maganar ana yin tane idan mutun yayi shairi kuma shairin ya komo masa.misali:shafiupac ya sa allura a katifa domin jammy ya hau ya taka sai da dare yayi har ya manta ya sa alluran sai ya kwanta saman alluran ta masa sukan dai dai.

7: Babu ruwan kwai da aski. ma'ana idan mutum bashi da alaka ta kusa ko nesa da abu kuma aka tambayeshi akan wannan abu sai ya ce babu ruwan kwai da aski kokuma babu ruwan biri da gada.

8 Kunfi kusa harshe da hakori