Kacici-kacici
Kacici-kacici tsarin wasa ne domin wasa kwakwalwa da kuma samun raha a kasar Hausa, sunayi ne domin ilimantarwa ko fadakarwa, kacici-kacici yana zuwa ne ta sigar zance a dunmule, amma wacce take kunshe da amsa, kuma ana bukatan masu sauraro da su bada amsa akan maganar.[1]
kacici-kacici | |
---|---|
game genre (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | puzzle (en) da word game (en) |
Bangare na | small genre of folklore (en) |
Has characteristic (en) | oral tradition (en) |
Tsari
gyara sasheKacici-kcici yana da alaqa da wasa kwakwalwa, amman galibi suna da bambamci, wasa kwakwalwa ana yinshi ta sigar tambaya ko magana a zube,wanda shima kacici-kacici haka yake,sai dai kawai kacici-kacici ana cewa “Kacici-Kacici” idan za ayi,shi kuma wasa kwakwalwa farawa kawai akeyi. Sannan ana cewa “kulin kulifita” wanda wannan magana ce wacce bata da ma’anata sigar furuci, amman tana da amsa domin hausawa na cewa “Gauta”.[2][1] “Gauta” alama ne dake nuna cewa zaka kasance cikin wasa.[2].
Misallai
gyara sasheI.Y yahaya (1988b) ya kawo su dayawa a cikin littafin shi,[3][4]
s/n | Kacici Kacici | Amsa |
---|---|---|
1 | Shanuna dubu madaurinsu daya. | Amsa: Tsintsiya |
2 | Baba na daka gemu na waje. | Amsa: Hayaki |
3 | Rigata daya aljihunta dari. | Amsa: Gidan Tururuwa |
4 | Tsumagiyar kan hanya Fyadi yaro fyadi babba. | Amas: Yunwa |
5 | Riga fari wando fari | Amsa: Balbela [5] |
6 | sauti, lafazi wajen yin wasan, misali: ƙurƙucif – ƙucif: | Amsa:Kwanciyar kare[6] |
Hikima
gyara sasheTana daga ciki hikimar tatsuniya, waƙa, kacici-kacici, fadakarwa, ilimantarwa da kuma nishadantarwa, amman galibin zancen a zukatan hausa alama ce na cewa wannan cikakken bahaushe ne, kanacewar akwai makwaftan hausawa dake yaran hausa a cikin su. Yanayin iya furta kalmomin da sanin zantukan karin magana, kacici-kacici da hikayu, alama ne na kasancewar mutum bahaushe ne, kuma iya furucin suna kiranshi da “Gagara Gwari” Ga daya daga cikin wasu furruci wadanda ake tankwara harshe, kuma cikakken Mallam bahaushe ne kadai yake iya yin furucin.( “Da kwado da kato suka tafi koto. Kato yai koto, kato ne zai kwace ma kwado koto, ko kuwa kwado ne zai kwace ma kato koto?”[6]
Hotuna
gyara sashe-
Littafin Kacici Kacici
-
Kacici Kacici a Makaranta
Bidiyoyi
gyara sashe- Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. ISBN 978-1-4744-6829-9. OCLC 648578425.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute.p,81
- ↑ 2.0 2.1 kraff 1976b.
- ↑ Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute.p.5
- ↑ Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute.p,8
- ↑ I.Y yahaya (1988b),(p251)
- ↑ 6.0 6.1 Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute.p,82