Kabir Mashi
Injiniya Kabir Ibrahim Mashi ya kasance tsohon shugaban ƙungiyar karɓan Haraji na Najeriya wato "Federal Inland Revenue Service" har zuwa shekarar 2015 lokacin mulkin shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya sauke shi, ya daura Samuel Ogungbesan. uma haifaffen jihar Katsina ne. Kuma Sarkin Katsina ya bashi sarautan "Kaigaman Katsina" a karkashin masarautar Katsina.[1][2][3][4]
Kabir Mashi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jahar Katsina, |
Sana'a |
Farkon Rayuwa
gyara sasheAn haifi Kabir Mashi a Karamar hukumar Mashi da ke jihar Katsina.[3]
Ilimi
gyara sasheKabir Mashi yayi karatunsa na digiri a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Sannan ya zarce zuwa Jami'ar Knightsbridge University, dake United Kingdom inda ya gama digirinsa na Mastas a Business Administration.[3]
Aiki
gyara sasheEngnr Kabir Mashi ya riqe matsayin Chairman na FIRS na wucin-gadi tsakanin shekara ta 2012 zuwa 2015.[5]An bashi sarautar Kaigaman Katsina a ranar 31 ga watan Mayu, shekarar 2015 a masarautar Katsina, wanda Sarki Abdulmuminu Usman ya nadashi. Alhaji Kabir Mashi memba ne na Chartered Institute of Taxation a Nigeria kuma har ila-yau yana cikin kungiyar "Association of National Accountants of Nigeria. Sannan ya kuma yi aiki a Water Board a Kaduna inda ya riqe matsayin Auditor General a 1984. Sannan yayi Chief Accoutant Pilgrims Welfare na Katsina a shekarar 1988. Sanan Director Finance & Supply a Ofishin Gwamnan Jihar Katsina a 1990. An bashi matsayin Director Board of Internal Revenue na Jihar Katsina a 1991, Chairman Katsina State Board of Internal Revenue.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.jiosaavn.com/song/kabir-mashi-kaigaman-katsina/KQdSZ0ZvTWk[permanent dead link]
- ↑ "Outgoing FIRS boss canvasses support for successor | Premium Times Nigeria". 2015-03-18. Retrieved 2021-06-01.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 3.3 "7 facts about 'Kaigaman Katsina', Kabir Mashi – Buhari's new appointee from Katsina". K.atsina Post. 2019-02-10. Retrieved 2021-06-01
- ↑ "Alhaji Kabir Mashi Archives". Hope for Nigeria. Retrieved 2021-06-02.
- ↑ "PressReader.com - Your favorite newspapers and magazines". www.pressreader.com. Retrieved 2021-06-01.