Ka'idojin rubutun hausa
kA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA Kamar yadda aka sani, kowanne lamari na duniya yana da ka'idar yadda ya kamata a gudanar da shi. Kuma bin ka'idar ita ke sa a sami dacen yadda ake bukata ba tare da an fuskanci wata matsala ba. Idan kuma ba a bi ka'idar ba a ga ba daidai ba. Tunda yake haka ne, rubutun Hausa shi ma, yana da ka'idarsa. Bin ka'idojin rubutun Hausa sau-da-kafa, su ke sa a sami rubutu mai Cikakkiyar ma'ana. Wato a sami daidaiton manufa tsakanin tunanain marubuci da kuma na makaranci.
ABUNDA AKE NUFI DA KA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA
gyara sasheKa'idojin rubutun Hausa, wani yanayi ne na lura da kiyaye ka'idojin harshen Hausa a rubuce domin samun damar isar da sakon da marubuci ke nufi zuwa ga mai karatu daidai da daidai, ba tare da canzawar ma'anar da marubuci ke nufi ba . Haka kuma, yana samar da saukin fahimtar karatu daga mai karantawa.
FANNONIN KA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA
gyara sasheFannonin ka'idojin rubutun Hausa da muke da su a nan, suna da dama. Kuma sune ginshin duk abinda ya kamata marubuci ya koya game da ka'idojin rubutun Hausa domin samun gwanancewa a rubutu. Don haka, zan zayyano su, sannan kuma na yi bayaninsu daki-daki kamar haka:
1- Alamomin ajiye magana; 2- Raba kalma da kuma hade kalma; 3- Yarda ake amfani da shaddatun bakaken Hausa; 4- Gajera da doguwar mallaka; 5- Dafa-keya 'w' da jakada 'w'; 6- Daurin 'm' da daurin 'n'; 7- 1.0 ALAMOMIN AJIYE MAGANA (punctuation mark)
Ga alamomin aje magana magana tare da bayanansu daki-daki:
1.1 Aya [.] Ita aya almar dugo ce, wace ake saka wa a cikin rbutu. Aya tana zuwa ne a karshen jimla, a lokacin da magana ta cika, sai a sami cikakiyar tsayawa a yayin karatu ko magana. Missali:
** A ranar da aka rantsar da sabon Shugaban kasar Najeriya Ahmad Bola Tunubu, ya ayyana janye tallafin man fetur. Sannan kuma, ya cigaba ba da zayyana wasu manufofin Gwamnatin tashi.**
idan an lura za a ga an sami ayoyi goda biyu a cikin missalin da na kawo. Wato daya a takiya daya a karshe. Amma duk da haka, ai kokarin tartan tantancewa domin wakafi ma, ya zo sau biyu a ciki. Idan an yi hattara sosai, shi ma sai ai la'akari da shi a missalin wakafi da zai zo nan gaba kadan.
1.2 Wakafi [,]
Wakafi, wata karmar tsayawa ce, wato dakatawa ko tsahirtawa wacce ba kai ta aya ba. Missali: "Na ga wani farin mutum jiya, sanye da faren kaya da jar hula, yana tsallaka titi a natse"
To a nan, za a ga an yi amfani da wakafi guda uku kafin aya da ta zo a karshe. Bayan hakka, ana samin wakafi yayin da ake zayyana wasu abubuwa. Missali:
- Wani Attajiri, ya rabawa mabukata kayan abinci kyauta a garin Gogori. Irin su shinkafa, masara, gero, wake, manja,sukari da sauransu.**
A wannan missalin za a ga yadda ake saka wakafi a tsakankanin abubuwan da aka raba. Wato shinkafa da masara da dawa, har zuwa karshe.
1.3 Ayar tambay [?] Ita almar ayar tambaya, alama ce da take fayyace jimlar da ke kunshe da tabaya. A yayain da marubuci yai nufin tambaya a cikin rubutunsa kuma bai sa wannan alama ba (?) To wannan jimla za ta tsaya ne a matsayin bayani maimakon tambya. Kuma, babu bukatar amsa domin ba a sa almar tambaya ba.Missali:
Aliyu ya zo?, menene ake sayarwa?
Idan aka yi lam'akari missalan da ke sama, za a ga an kawo jimloli guda biyu kuma dukkanin suna dauke da alamar tambaya. Bayan haka, a duba kasa za a ga an sake maimaita jimlar farko ba tare da alamar tambaya ba:
Aliyu ya zo
A nan za a fahimci cewa ana yin bayanin cewa Aliyu ya riga har ya zo wani wuri ne, maimakon tambaya akan zuwan Aliyu wani wuri.
1.4 Aya mai ruwa/ Ruwa biyu [:] Wannan wata alama ce da ta ke alamata nuni da zuwan wasu abubuwa a kasa, haka kuma ana amfani da su waje fayyace awanni, minting da kuma sakanni na lokaci. Missal:
A= 12:56 (wato karfe sha biyu da minti hamsin da shida) B= Missali na biyu a duba duk inda na ce MISSALI za a ga na yi wannan alamar [:] sannan a ga missalan sun biyo baya. To wannan ma na daya daga cikin amfanita C= idan an zo zayyana wasu abubuwa, akan yi amfani da wannan alama ta Ruwa-biyu. Kamar a ce, Shugaban kasa zayyana wasu manufofin Gwamnatinsa guda uku da tasa a gaba kamar haka; Inganta noma da kiwon dabbobi; Yaki da cin hanci da rashawa; Samar da isasshen man fetur; da sauransu.
A nan idan aka lura sosai, za a ga sai da na sa alamar ruwa-biyu [:] sannan na kawo wadancan abubuwa uku da aka ce Shugaban kasa ya zayyana.
1.5 Wakafi mai ruwa [;] wannan alama ce da ake amfani da ita wajen raba jerin wasu jimloli ko kalmomi a cikin zance. Game da missali, a duba a missalin karshe na Aya mai ruwa , za a ga yadda aka bayyana abinda Shugaban kasa ya zayyana. A nan za a ga an sa Ka alamar (;) a gaban kowacce jimla. Ga Karin missali: A= Shugqban makarantar ya gargadi dalibai cewa,idan sun tashi dawowa daga hutu, su zo da kayan karatu kamar idan haka:
1 littafin koyon turanci, aji na biyar; 2 littafin koyan lissafi, aji na biyar; 3 littafin nazarin rayuwar dan Adam, aji na biyar; 4 littafin koyan karatn Hausa, aji na biyar.
A wadannan missalai za a lura cewa, a duk karshen jimloli 3 na farko an saka alamaar tsayawa ta wakafi mai ruwa (;), in banda jimla ta karshe da aka yi wa alamar aya (.)
1.6 Alamar Zarce [-] Zarce, alama ce da ake amfani da ita wajen hade kalmomi biyu ko sama da biyu, su zama kalma daya da ma'ana daya. Akan saga wannan alama a takanin kalmomi da suka zo iri daya ko wadanda suka zo daban-daban. Kin saka wannan alama a inda ya dace, yakan kawo sabanin ma'ana. Missali:
1 malam-buda-mana-littafi (sunnan wani kafilfilo); 2 fadi-ka-mutu (tangaran); 3 fari-fari (abinda bai kai fari sosai ba); 4 malfar-ungulu (wani tsiro ne); dss.
A lura da kyau, idan muaka dauki missali na farko, (malam-buda-mana-littafi) za mu ga yana nufin sunan wani abu wato, kafilfilo. Idan kuma ba a sa wannan alama ba a tsakankanin kalmomin (malam buda mana littafi) to rubutun ya zama wata jimla mai nufin umarni. Wato, dalibai ne ke umartar malaminsu da ya buda masu littafi.
1.7 Alamar zancen wani [" "].Wannan alama ce da marubuci yake amfani da ita wajen nuna maganar wani mutun kai-tsaye. Wato a nan mawallafi ko marubuci zai Bude maganar wani ta kai-tsaye da wannan alamar ["], sannan idan magaanr ta zo karshe sai ya rufe da irin wannan alamar ["]. Ga missqli kamar haka:
1 A yayin da 'yanjaridu suke ganawa da shugaban kasar, ya dau alkawari na inganta rayuwar al'ummar kasar tashi. Har ma yake cewa: "Ya ku al'ummar wannan kasa tamu mai cike da albarka. Ina yi maku albishir da cewa, daga yau na sauke farshin man fetur da kaso hamsin cikin dari (50%). Bayan haka kuma, zan raba wa Manoma takin zamani da sauran kayan aikin gona kyauta domin farfado da tattalin arzikin kasar nan". A wannan dan missali da ke sama, za mu fahimci yadda aka bayyana jawabin Shugaban kasa kai tsaye.
1.8 Alamar baka-biyu ( ). Wannan wata alama ce da ake amfani da ita wajen nuna karin bayani akan wata kalma ko a kan wani abu.