KYAUTA A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI.
KYAUTA A MAHANGAR ADDININ MUSULUNCI.
gyara sasheAl’amarin kyauta a mahangar addinin Musulunci, ana iya cewa baiwa ce, kuma ibada ce muhimmiya. Bisa dalilin muhimmancinta yasa Allah (S.W.T) yayi ummarni da yin kyauta. A daya bangaren, sai aka kwadaitar da yawaita kyauta tare da bayyana fa’idojin da kyauta ke jawowa wanda ya yi ta. Akwai ayoyi da yawa wadanda aka tsoratar da yin rowa, tare da nuna illolin da take jawo wa mai yinta, watau marowaci.
Bayan ayoyin qur’ani kuma, akwai hadisai masu yawa da suka nuna muhimmancin kyauta. A musulunci an kira kyauta (bayarwa) da sunaye daban daban kamar: zakka da zakkatul fitir (zakkar kono) da imfaki(ciyarwa) da wakaf (bayar da gida ko gona ko makaranta) da wasiyya da layya da hadaya da sauransu.
Kyauta Da Sadaka
Kyauta da Sadaka suna da kusanci da juna matuka don sun yi kama, sau da yawa abin dake bambanta su ita ce niyya.
Manzon Allah (SAW) yana kar:ar kyauta, amma ba ya karbar sadaka. Bukhari 3.751.
Manzon Allah (SAW) ya tabbatar cewa kar a bai wa iyalan gidan Muhammad sadaka. Muslim ya rawaito.
Abu Huraira ya ce: wata rana Hassan ya dauki kwayar dabino. Manzon Allah ya ce kai fito da shi ba ka san mu ba ma cin sadaka ba? Fikhus sunna 3.73B
An taba bai wa Barira sadakar nama, amma ta kawo wa Annabi (SAW), sai Annabi ya ce: ke sadaka a gareki mu kuma ya zama kyauta. Bukhari 2.571.
Daga Abu Huraira ya ce: "Idan aka kawo abinci zuwa ga Manzo Allah(SAW), yakan tambaya cewa kyauta ko sadaka? Idan aka ce sadaka ce, sai ya ce Sahabbai su ci, amma in aka ce kyauta ce, sai ya ci tare da Sahabbai. 3.750.
Zakkah: Sadaka (kyauta) ce ta wajibi watau ita farilla ce, amma ga mai wadata.
Sadakatul Jariya: Manzon Allah (SAW) ya ce: Idan mutum ya mutu dukkan ayyukansa sun yanke. In ban da ayyuka uku, sadaka mai gudana da ilmin da ya koyar ake aiki da shi, sai kuma natsattsen Da wanda zai rinka yi masa addu’a. Fikhus Sunna 104 A.
Daga Anas Bin Malik ya ce: Duk wanda ya dasa bishiya ko ya shuka dan itace ya tsira ya yi Yaya , wani tsuntsu ko dabba ko mutum ya ci daga gareta. Wannan kamar sadaka ce mai gudana.Bukhari 3.513
Shari’ar Musulunci ta shardanta wasu hukunce-hukunce don ladabtarwa, a inda ta yanke cewar a ciyar da abinci (kyauta) ko a yanta baiwa. Kamar wajen kaffarar azumin watan ramadana, inda aka ce duk wanda ya karya azumi da gangar, sai ya yi azumi sittin, ko ya yanta baiwa, ko ya ciyar da mutane sittin. Wannan ciyarwa alama ce ta kyauta wadda yake kishiyar rowa ce, don haka Musulunci ba ya son Musulmi ya zama marowaci.
Bayan wannan kuma sai kaffarar rantsuwa, nan ma ko dai mutum ya yi azumin kwana uku, ko ya ciyar da mutane goma abincin da zasu koshi.
Bayan wannan tsari kuma, sai bangaren da aka umarci Musulmai dasu yi kyauta, subada zakka da sadaka da wakafi. Dukkan wadannan suna korar ko kawar da rowa a tsakanin Musulmai.
Sada Zumunci Da Kyauta
Ana iya sada zumunci ta hanyar yin kyauta, zumuncin zai iya kasancewa naka ko na waninka. Bayan haka kuma zai iya faruwa a tsakanin mutane rayayyu (masu rai) da matattu (wadanda suka rasu). Haka iyaye ko mata ko yayye da sauransu.
“Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). Ya kasance ya rinka bayar da kyauta zuwa ga kawaye Khadija matarsa ta farko ko bayan da ta rasu. A’isha (R.A.) ta riwaito cewa: “Ban taba jin kishin wata mata daga cikin matan Manzon Allah ba, kamar yadda nake kishin Khadija, duk da yake ban taba ganinta ba.
Manzon Allah yakan yawan tuna ta tare da ambatonta, kuma in ya yanka rago yakan Debi naman ya bayar ya ce a kai wa wasu daga kawaye Khadija. Wata rana na taba ce masa ka damu da Khadija matuka, tamkar ba wata mace a Fadi duniyar nan sai Khadija. Yace: “ Khadija ta yi min komai a rayuwa wanda ba wani da ya yi min kamar haka, sannan daga gareta na samu Yaya ”. Bukhari 5.166.
Akwai wani bayani wanda ya faru a zamanin Sahabbai, inda Abdullahi Ibn Umar zai tafi aikin hajji. Suna cikin tafiya da jama’arsa, sai suka hadu da wani Balaraben kauye. Abdullahi Ibn Umar nan da nan, sai ya dauki abin hawansa da jabba ya ba shi, sannan kuma ya girmamashi. Bayan sun rabu sai aka tambayi Ibn Umar game da wannan mutumin, sai Ibn Umar yace:
"Mahaifin mutumin abokin Sayyidina Umar Bin Khaddaf ne”. Ibn Umar ya Kara da cewa: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “ku sadar da zumuncin da iyayenku suke yi suna raye ko bayan sun rasu”.
Kyauta Ga Makwabta:
A’isha ta ce: “Ya Manzon Allah, ina da makwabta biyu wane zan bai wa kyauta daga cikinsu? Manzon Allah ya ce: “ki bai wa wanda kofarsa ta fi kusa da ke. Bukhari. 3.767
A’isha (R.A.) ta riwaito cewa: Manzon Allah yana yanka akuya ya rarrabar da naman, sai ya tambaya ko akwai abin da ya rage?A’isha ta ce saura karfata, sai Annabi ya ce nama na nan, karfata ce aka rasa.Tirmizi ya riwaito.
Ladubban Kyauta a Musulunci:
Kyauta na da wasu ladubba wadanda shari’a ta tsara don al’umma su kiyaye. Akwai na umarni da kuma na hani da na kwadaitarwa da na tsoratarwa da sauransu.
Abubuwa Da Suke bata Kyauta Ko Sadaka
Akwai wasu abubuwa wadanda mutum zai yi su bata masa kyauta ko sadakar da ya yi. Da farko akwai riya ko gori ko zobe ko tasau da sauransu.
Riya
Na nufin ka yi wa mutum kyauta ko sadaka ba wanda ya sani, ka zo kana bayar da labari don a yaba maka. Tabbas riya na bata aiki komai yawansa.
Gori
Na nufin ka yi wa mutum kyauta ko sadaka, amma daga baya ka rinka cewa, ashe ba na yi maka kaza da kaza ba? Hakika gori na bata kyauta ko sadaka saboda tana tozarta wanda aka yi wa. Wannan ya sa Manzon Allah ya hana, Allah (swt) Ya hana a cikin Alqur’ani a inda Yace: “kar ku bata sadakar ku da gori da zobe”
Zobe
Na nufin ka yi wa mutum kyauta ko sadaka, amma daga baya ka kwace abin da ka bayar. Wannan shi ma shari’a ta hana, saboda ta haifar kiyayya a tsakanin wanda aka yi wa kyauta ko sadaka da wanda ya yi.
Bisa kyakkyawar dabi’a duk wanda ya aikata wannan ana daukarsa karamin mutum. Bisa shari’a kuwa, shi ma wannan abin kyama ne. Akwai wani hadisi mai yin haka ya yi kama da kare. Domin kare ya ke yin amai sannan daga baya yana dawo ya lashe abisa.
Tasau
Na nufin mutum ya yi wa budurwa ko bazawara toshi (kyauta). Bayan ya yi mata toshi sai daga baya ya tayar da kyautar wato ya kwace. Bisa kyakkyawar dabi’a duk wanda ya aikata wannan ana daukarsa karamin mutum ma’ana mai karanta. Duk wanda aka san shi wannan hali ba ya yin farin jini a gari. Bugu da kari Yanmata kan guje shi.
Raina Kyauta
A al’adance an hana mutum ya raina kyautar da aka yi masa, saboda Bahaushe ya ce: “maraina kaɗan ɓarawo ne”, ko “lomar hasafi ta fi kaɓakin tsiya” ko “da babu gara ba dadi”.
Haka kuma ko a musulunce shari’a ta hana raina kyauta kamar a wani hadisi inda Abu huraira ya ce:Manzon Allah ya ce: “ya ku mata kar daya daga cikin ku ta raina kyautar da kawarta ko makwabciyarta ko da kofatan akuya ne”.Bukhari 3.740
Daga Abu huraira ya ce: Manzon Allah Ya ce: zan amsa gayyata walima ko da abincin kofaton akuya ne.
KYAUTAR DA MUSULUNCI KE KYAMA.
Abdullahi bn Umar da Abdullahi Abbas sun ruwaito cewa: Manzon Allah (SAW) haramun ne mutum ya bayar da kyauta ko sadaka, sannan daga baya ya zo ya kwace, sai tsakanin uba in yaba dansa. Duk wanda yayi kyauta ya koma mata ya zama kare mai yin amai ya dawo lashe. Abu Dauda 1571.
Abu umama ya ruwaito cewa: Manzon Allah yace "duk wanda ya taimaki dan uwansa sannan ya karbi wata kyauta daga gare shi to tinkari wata kofa daga kofofi riba (rashawa). 1573
Abdullahi bn Ammar bn As ya ce: Manzon Allah ya ce: ba a yarda ba mace ta yi kyauta da wani abu daga kayan mijinta ba, sai da izininsa. Abu Dauda 1575.
Nu’uman bn Bashir yace: Babansa ya tafi da shi wajen Manzon Allah, ya ce: Na baiwa Dana bawa, sai Manzon Allah ya tambaya ka bai wa sauran Ƴaƴanbka kamar haka? Sai ya ce: a’a, Manzon Allah ya ce: karɓi kyautarka. Bukhari3.759.
A karshe, ga wasu karin hujjoji kadan don a sanya su a matsayin madogara. Wadannan hujjoji sun kunshi ayoyin Kur’ani da wasu hadisai, da kuma maganganun wasu bayin Allah.
Gaba Dayansu sun yi nuni ne ga fa’idar bayarwa (kyauta ko sadaka ko zakka) a Musulunce da kuma cewa bayarwa ibada ce ga mahangar Musulunci. Bayan haka kuma baiwa ce domin kuwa sai wanda Allah Ya yarda da shi yake yin alheri.
An ambaci sadaka Suratul Baƙara aya ta 219, 270, 272, 274, 291, Ala’imrana aya ta 92, 134, Nisa’I aya ta 114, Tauba aya ta 60, 79, 103, Nur aya ta 56, Mujadala aya ta 12, 13,
An yi ummarnin yin sadaka a Suratul Bakara aya ta 271,
An ambaci fa’idoji da falalar sadaka Suratul Bakara aya ta 261, Anfal aya ta 60, Suratul Hadid aya ta18, Tagabun aya ta17.
An tsoratar a kan kin yin sadaka Suratul Suratul Isra’il aya ta 28, ayoyi da surori masu yawa a Kur’ani mai girma :
Suratul Isra’il aya ta 29. Kar ka make hannunka ka zama marowaci, kar kuma ka zama almubazzari don kar ka zama abin zargi, ko ka talauce.
A cikin Suratul Laili. Da Suratul Ma’uun, da cikin Suratul Hadid.
Abu Huraira ya ruwaito Annabi ya ce: “mai kyauta yana kusa da Allah, kuma kusa da Aljannah, kuma kusa da mutane. Amma marowaci kuwa yana nesa da Allah, kuma yana kusa da wuta. Jahili wanda yake yin kyauta ya fi kusa da Allah fiye da mai ibada marowaci. Tirmizi: 580:
Aliyu Dan Abi Dalib yace: Malami saboda iliminsa yana iya zama mai kyauta. A inda mai dukiya saboda son dukiyarsa yana iya zama marowaci.
A Musulunci, an fifita mai bayar da kyauta a kan wanda yake karba. kamar wani hadisi dayace: Hannun sama (Mai bayarwa) yafi hannun kasa (mai kar~a) daraja. Duk wannan ana nuna kyawun kyauta fiye da rowa da kuma kwaɗayi.
Ibn Abbas ya ce, Manzon Allah shi ne mafi alheri (Kyauta) a mutane. Ya fi yin kyauta a watan azumi, ya fi iska kyauta.1.1
Abdullahi Bin Amr ya ce, wani mutum ya tambayi Annabi cewa: Wane aiki ne ya fi a musulunci? Sai ya ce ka ciyar da talaka, sannan ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba. Bukhari 1.11.