Josip Iličić ( Croatian pronunciation: [jǒsip ǐlitʃitɕ] ; an haife shi ne a ashirin 29 ga watan Janairu shekarai alif dari tara da casain da takwas 1988) ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne na Slovenia wanda ke taka leda a matsayin mai gaba ga ƙungiyar Slovenia PrvaLiga Maribor .

Josip Iličic a wasan da sukayi da leece watan Maris shekarai 2020

Iličić ya fara aikinsa da manyan yan wasa na ƙwararru tare da qungiyar din Slovenia Bonifika, daga baya kuma yana taka leda a Interblock da Maribor a ƙasarsa, kafin ya koma qasar Italiya a shekarai dubu biyu da goam 2010 don shiga Palermo . A cikin 2013, ya rattaba hannu kan Fiorentina, daga baya kuma don Atalanta a cikin 2017. Bayan ya shafe shekaru goma sha biyu a Italiya, Iličić ya koma Maribor a 2022.

Ya ji daɗin mafi kyawun lokacinsa a matsayin ɗan wasan ƙwallon ƙafa cikin wanda suka fi kowa oyawa tare da Atalanta a qasar italiya, yana zira kwallaye goma sha ɗaya ko fiye a cikin kowane shekaru uku na farko a ƙungiyar tasa kuma an ba shi wuri a cikin shekarai 2018 – 19 Serie A Team of the Year . Shi ne dan wasa na farko da ya zura kwallaye hudu a waje a gasar cin kofin zakarun Turai, sannan kuma shi ne dan wasa mafi tsufa da ya ci kwallaye hudu a gasar cin kofin zakarun Turai.

Iličić ya fara buga wa babbar tawagar kasar Slovenia wasa a watan Agustan shekarai dubu biyu da goma 2010 a wasan sada zumunci dasuka fafata da Australia . Shekaru uku bayan buga wasansa na farko, ya zura kwallonsa ta farko a gasar cin kofin duniya dasuka fafata da qasar kasar Cyprus a watan Satumban 2013. Gabaɗaya, ya buga wasanni 79 a ƙungiyar a cikin aikinsa na shekara goma sha ɗaya.

Aikin kulob gyara sashe

A ranai ashirin da uku 23 ga watan Yuli shekarai 2013, Palermo bisa hukuma ta tabbatar da siyar da Iličić ga abokan hamayyar Serie A Fiorentina a qasar italiya akan gidan yanar gizon su. Daga baya, Fiorentina ta qasar italiya ta sanar da yarjejeniyar a hukumance akan gidan yanar gizon su. Ba a bayyana kudin canja wurin ba, an ruwaito cewa yana cikin jimlar Yuro miliyan tara 9 ciki har da wanda ake qarawa add-ons. Ya zura kwallaye shida a kakarsa ta farko a Fiorentina. 2014-15 kakar ya kasance mafi nasara a gare shi, yana gamawa a matsayin babban dan wasan kulob din tare da kwallaye goma a duk gasa, tare da Mario Gomez .