Josef Kumbela

Jarumi kuma daraktan fim

Joseph Kumbela (an haife shi a shekara ta 1958) ɗan wasan kwaikwayo ne kuma mai shirya fina-finai daga Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango wanda ya sami lambobin yabo dalilin wasan kwaikwayo.

Josef Kumbela
Rayuwa
Haihuwa 1958 (65/66 shekaru)
ƙasa Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango
Sana'a
Sana'a darakta
IMDb nm0474950

Rayuwa da aiki

gyara sashe

An haifi Joseph Kumbela a shekara ta 1958. Ya taso a ƙasar Switzerland tun 1980. Ya fara aikinsa a matsayin ɗan wasan kwaikwayo a Faransa da Amurka. A lambar yabo ta FESPACO a shekarar 1993 ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan kwaikwayo saboda rawar da ya taka a cikin wasan barkwanci mai suna Gito l'ingrat (Gito the ungrateful) wanda Leonce Ngabo na Burundi ya jagoranta/bada Umarni. A cikin wannan fim ɗin Gito, ɗalibi daga Burundi kuma ƙwararren mai ba da shawara a Paris, ya yanke shawarar komawa gida. Tare da takardar shaidarsa a hannu da kuma cike da tsare-tsare game da aikinsa, ya bar abokiyar aikinsa Faransa Christine yana alkawarin kawo ta Burundi daga baya. Ba zai iya samun aiki ba, amma ya sadu da tsohuwar masoyiyar yaransa. Daga nan Christine ta zo ba tare da gargadi ba kuma ta gano abin da ke faruwa. Matan biyu suka haɗa kai don koyar da Gito darasi.[1]

Josef Kumbela ya rubuta kuma ya ba da umarni ga gajerun fina-finai tun 1994 ta hanyar amfani da kamfaninsa na samar da kayayyaki na Geneva. Fim ɗinsa na 1998 L'étranger venu d'Afrique (Baƙo daga Afirka, ko Feizhou Laowai) shi ne fim ɗin Afirka na farko da aka yi a China. Ya na bayar da labarin wata soyayya tsakanin Lulu, wata daliba ƴar Afirka, da wata ƴar ƙasar Sin, kuma ya nuna yadda al'adu suka yi arba da juna.

Shekara Suna Matsayin Bayanan kula
1998 L'Étranger venu d'Afrique - FEIZHOU LAOWAI Director, Writer 13 minutes. Comedy
1996 Colis Postal Director 10 minute comedy
1996 Taxcarte Director, Actor 7 minute comedy
1994 Perle Noire Director, Writer 27 minute comedy drama
1992 Gito, l'ingrat Actor 90 minutes. Comedy
Entre-Deux Director 90 minutes. Comedy Drama
1990 In the Eye of the Snake Actor 90 minute thriller

Manazarta

gyara sashe
  1. "GITO L'INGRAT". Cine Trois Mondes. Archived from the original on 2020-11-06. Retrieved 2012-03-19.

Hanyoyin Hadi na waje

gyara sashe