Jomo Kenyatta a shekara ta 1966.

Jomo Kenyatta ɗan siyasan ƙasar Kenya ne. An haife shi a shekara ta 1897 a Gatandu, Kenya (a lokacin mulkin mallakan Birtaniya); ya mutu a shekara ta 1978 a birnin Mombasa. Jomo Kenyatta firaministan ƙasar Kenya na farko ne, daga watan Yuni a shekara ta 1963 zuwa watan Disamba a shekara ta 1964, da shugaban ƙasar Kenya na farko ne daga watan Disamba a shekara ta 1964 zuwa watan Agusta a shekara ta 1978 (kafin Daniel arap Moi).

ManazartaGyara

Wannan ƙasida guntu ne: yana buƙatar a inganta shi, kuna iya gyarashi.