Johnson O. Akinleye
Johnson O. Akinleye shine shugaba na goma sha biyu na Jami'ar North Carolina Central University. An naɗa shi a matsayin chancellor na jami'a a ranar 26 ga watan Yuni, 2017.[1]
Johnson O. Akinleye | |
---|---|
Rayuwa | |
Karatu | |
Makaranta |
Alabama Agricultural and Mechanical University (en) Howard University (en) |
Sana'a | |
Employers |
Bowie State University (en) (1986 - 1989) North Carolina Central University (en) (26 ga Yuni, 2017 - 30 ga Yuni, 2024) |
Mamba |
Omega Psi Phi (en) Sigma Pi (en) |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Johnson O. Akinleye 1 daga cikin yara 22 a Ile-Ife, Najeriya. Ya sami digiri na farko a fannin sadarwa da kuma digiri na biyu a fannin fasahar watsa labarai daga Jami’ar Alabama A&M da digirin digirgir a fannin ilimin sadarwar ɗan Adam daga Jami’ar Howard.[2]
Sana'a
gyara sasheAkinleye ya fara aikinsa a matsayin mataimakin farfesa a Sashen Sadarwa a Jami'ar Jihar Bowie daga shekarun 1986 zuwa 1989. Kafin zuwan NCCU, ya rike muƙamai a Jami'ar Bethune-Cookman, Kwalejin Edward Waters, da Jami'ar North Carolina Wilmington. Akinleye ya shiga NCCU a shekara ta 2014 a matsayin provost kuma Vice-chancellor kan harkokin ilimi. Ya yi aiki a matsayin mukaddashin chancellor na NCCU daga watan Agusta zuwa Disamba 2016, kuma a matsayin chancellor na wucin gadi daga watan Disamba 2016 zuwa Yuni 2017, lokacin da ya sami naɗin na dindindin bayan mutuwar Debra Saunders-White. Dr. Akinleye sau da yawa ana yi masa laƙabi da jagorancin sa da bunƙasa jami'ar sa ta zama babba mai nagarta na HBCU.[3] Ya kasance fitaccen mai magana akan PBS.[4] An naɗa Dr. Johnson O. Akinleye a kungiyar NCAA Division I Presidential Forum.[5]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheAkinleye ya auri Juanita Akinleye. Suna da yara biyu manya (Nikki da Peter). Akinleye memba ne na Omega Psi Phi da Sigma Pi Phi fraternities.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Johnson O. Akinleye Elected 12th Chancellor of North Carolina Central University". Los Angeles Sentinel (in Turanci). 2017-07-14. Retrieved 2020-09-01.
- ↑ "Johnson O. Akinleye, Ph.D. | North Carolina Central University". www.nccu.edu. Retrieved 2020-09-01.
- ↑ Spotlight-Dr. Johnson O. Akinleye
- ↑ Focus on Johnson O. Akinleye, PH.D - Chancellor of North Carolina Central University
- ↑ NCCU Chancellor Appointed to NCAA Division I Forum