Jini bayan haihuwa
Sau da yawa ana bayyana jini bayan haihuwa a matsayin rasa fiye da milimita 500 ko milimita 1,000 na jini bayan haihuwa.Wasu sun daɗa cewa akwai alamun da ke nuna cewa akwai karancin jini, Da farko, alamun sun haɗa da: tashin zuciya, rashin jin daɗi sa'ad da jinin ya tsaya, da kuma ƙarin ɗaukan numfashi. Yayin da jini ya ƙara ƙarewa, macen data haihu zata iya fuskantar jin sanyi, ƙarfin zubar jinin zai iya raguwa, Wannan yanayin zai iya faruwa har mako shida bayan mace ta haihu.
Dalili mafi yawa shi ne rashin ƙarfin mahaifa bayan haihuwa,Zubar ciki, ko kuma rashin jini, Yana faruwa da yawa a waɗanda: da yake suna da karancin jini, ' yan kasar Asiya ne,matan da suke da kiba ko fiye da jariri ɗaya a ciki, ko matan da suka wuce shekara 40.Zubar jini na faruwa ne da yawa idan anyi ma mace fida an fiddo jariri daga ciki.
Kawar da hakan ko kuma mafita ya ƙunshi rage abubuwa da aka sani cewa za su iya jawo haɗari, har da yadda ake yi wa wannan yanayin, idan zai yiwu, da kuma ba da damar yin amfani da magunguna don ya motsa ciki ba da daɗewa ba bayan an haifi jaririn.
Ma'ana
gyara sasheDaidai da tushen, ana bayyana jini bayan haihuwa a matsayin jini fiye da milimita 500 bayan haihuwar ciki ko milimita 1,000 bayan yin fida a cikin sa'o'i 24 na farko bayan haihuwar. Jini na biyu bayan haihuwa shi ne wanda yake faruwa bayan rana ta farko da kuma makonni shida bayan haihuwa.
Alamomi
gyara sasheAlamomin sun ƙunshi zubar jini mai tsanani daga cikin ciki da kuma jinkiri ko kuma daukan lokaci mai tsawo,da kuma karuwar bugun zuciya, yayin da ake fuskantar zubar jini, mai ciwon zai iya jin sanyi, ƙarfin jini zai iya rage,da kuma fitar hayyaci.