Iyi-uwa
Iyi-uwa wani abu ne daga tatsuniyar Ibo da ke daure ruhin yaron da ya mutu (wanda aka fi sani da ogbanje) ga duniya,ya sa ya dawo ya sake haifuwa ga uwa daya.
Iyi-uwa |
---|
Abubuwa da yawa na iya cika manufar iyi-uwa,gami da duwatsu,tsana, gashi ko guntuwar tufafin yaron da ya mutu,alamu,ko hadaya.Dole ne a nemo iyi-uwa a lalatar da shi domin ogbanje ya huta,ya daina addabar uwa.Don gano abin,shamans da aka fi sani da 'dibia' suna tambayar ruhin kuma suna yin al'ada don tilasta shi ya bayyana inda iyi-uwa yake.
Littafin novel Things Fall Apart na marubucin ɗan Najeriya Chinua Achebe yana ɗauke da cikakken shirin da ya shafi ɗan oganje da iyi-uwa.[1]
- ↑ Things Fall Apart by Chinua Achebe