Issa Obalowu Aremu (an haife shi 8 ga watan Janairun 1961) ɗan gwagwarmaya ne kuma shugaban ƙwadago na Najeriya. Shi ne babban sakatarenkungiyar ma'aikatan masaka da tufa da ɗinki ta Najeriya (NVTGTWN) kuma mataimakin shugaban ƙungiyar masana'antu ta duniya.[1] Kwamared Issa Aremu mamba ne a majalisar zartarwa ta ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, kuma ya taɓa zama mataimakin shugaban majalisar a zamanin Adams Oshiomole.[2]

Isa Aremu
Rayuwa
Haihuwa 8 ga Janairu, 1961 (63 shekaru)
Sana'a

Sana'a gyara sashe

Aremu ya halarci makarantar firamare ta Ilorin kuma ya kammala karatunsa na sakandare a Ilorin Grammar School, Oko erin, Garin Alimi, Ilorin, jihar Kwara. Aremu ya kammala karatunsa na B.sc a fannin tattalin arziƙi a Jami'ar Fatakwal, jihar Rivers a shekarar 1985.[3] Shi tsohon ɗalibi ne na George Meany Labour Centre, Maryland, Washington, Amurka kuma yana da digiri na biyu a kan Lada da Ci gaba daga Cibiyar Nazarin Zamantakewa, ISS, a Hague, Netherlands. Aremu ya shiga ƙungiyar ƙwadago ne a matsayin shugaban Sashen Tattalin Arziƙi/Research na NLC. Aremu ya shiga ƙungiyar ƙwadago ne a matsayin shugaban Sashen Tattalin Arziƙi/Research na NLC. A watan Agustan 1989, ya shiga NUTGTWN kuma ya zama Babban Sakatare a cikin shekarar 2009.[4][5] Ya kasance wakilin ƙwadago a babban taron ƙasa da aka gudanar a 2014 kuma ya zama mataimakin shugaban kwamitin taron ƙasa kan ƙungiyoyin jama'a, ƙwadago, matasa, da wasanni.

Siyasa gyara sashe

A ranar 18 ga watan Yunin 2018, ya bayyana ƙudirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Kwara a dandalin jam’iyyar Labour a zaɓen 2019 mai zuwa.[6][7]

Rayuwa ta sirri gyara sashe

An haifi Aremu a ranar 8 ga watan Janairun, 1961 a Ijagbo a wajajen Oyun, Jihar Kwara, ga Mahamudu Aremu da Hadjia Afusatu Amoke Aremu. Kwamared Issa Aremu ya auri Hadjia Hamdalat Abiodun Aremu, wacce ta rasu a watan Disambar 2015. Yanzu haka yana auren Khadijat Aremu.[8][9]

Manazarta gyara sashe

  1. https://www.industriall-union.org/industriall-global-union-elects-new-leadership
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-02-17. Retrieved 2023-03-17.
  3. https://www.vanguardngr.com/2018/07/aremu-joins-kwara-governorship-race/
  4. https://www.channelstv.com/2016/01/13/textile-workers-criticise-18000-naira-minimum-wage-reduction/
  5. nutgtwn.org/?page_id=17
  6. https://punchng.com/issa-aremu-declares-bid-for-kwara-governorship/
  7. https://www.premiumtimesng.com/regional/north-central/277021-2019-labour-leader-issa-aremu-declares-to-run-for-kwara-governor.html
  8. https://www.vanguardngr.com/2015/12/labour-leader-issa-aremu-laments-wifes-death/
  9. https://web.archive.org/web/20150927114155/http://www.dailytrust.com.ng/news/general/comrade-issa-aremu-loses-mother/112359.html