Ambassador Iro Ladan Baki[1] (An haifeshi ranar 10 ga watan Yuli, 1953) a birnin Katsina, Najeriya. Ya fito ne daga dangin Sarki Muhammadu Dikko[2] kuma yayi aiki a kasashe da dama da suka hada da Indiya da Turkiya. An bashi matsayin Jakada Najeriya a kasashen Hague da Netherlands inda ya zamo jam’in mafi kananan shekaru da ya rike wannan matsayi a Najeriya.[3]

Iro Ladan Baki
Rayuwa
Haihuwa Katsina, 10 ga Yuli, 1953
Mutuwa 1991
Sana'a

Kuruciya da Ilimi gyara sashe

An haife Ladan Baki a Katsina a ranar  10th July 1953 da iyalin Alhaji Usman Ladan Baki na tsatson Sarki Muhammadu Dikko. Ya fara karatunsa a gida daga bisani a Provincial Secondary School dake Zaria (a yanzu Alhuda-huda College, Zaria) tsakanin 1956-1959,[3] sannan kuma Government College da ke Kaduna a 1970. Ya sama digirinsa na farko a A.B.U Zaria a tsakanin shekarun 1971-1975.[3]

Aiki gyara sashe

Ya fara aikinsa na gwamnati a Ma’aikatun kasashen waje a matsayin jami’in kasa da kasa. Yayi aiki a kasashe sa dama da suka hada da Indiya da Turkiya. An bashi matsayin Jakada Najeriya a kasashen Hague da Netherlands (Satumba, 1987) inda ya zamo jam’in mafi kananan shekaru da ya rike wannan matsayi.[3]

Rayuwa gyara sashe

Baki ya kasance yana da 'ya'ya hudu, biyu maza biyu mata.

Mutuwa gyara sashe

Baki ya rasu a shekarar 1991 kuma an birne shi a Katsina a bisa tsarin addinin musulunci.

Manazarta gyara sashe

  1. lastnames.myheritage.comhttps://lastnames.myheritage.com/last-name/Ladan+Baki. Retrieved 2022-06-23.
  2. "Dandalin Tarihin Magabata - Jikokin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko; Ladan Fari da Ladan Baki rike da wani tsuntsun ruwa da ake kira Penguin. Anyi hoton a wani gidan dabbobi dake birnin London, cikin shekarar 1924. Abin mamaki wannan tsuntsu baya tashi. Ko hakan nada nasaba da kasancewar fiffikensa karami? Shin yaya sunansa da Hausa? Mudai bamu sani ba, ayi mana uzuri. | Facebook". hi-in.facebook.com (in Hindi). Retrieved 2022-06-23.
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 Adeolu (2017-03-24). "LADAN-BAKI, Amb. Iro". Biographical Legacy and Research Foundation. Retrieved 2022-06-23.