Immaculate Ndabaneze (an haife ta a shekara ta 1972) minista ce a Burundi. Ta yi aiki a matsayin ministar kasuwanci, sufuri, masana'antu da yawon buɗe ido daga watan Yuni 2020 zuwa watan Mayu 2021 kafin a kore ta sakamakon ikirarin almubazzaranci. [1] [2] [3] [4]

Immaculate Ndabaneze
Minister of Commerce, Transport, Industry and Tourism (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa 1972 (51/52 shekaru)
Sana'a
Sana'a civil servant (en) Fassara

Tarihi da aiki

gyara sashe

Ndabaneze 'yar asalin Gihanga Commune ce a lardin Bubanza. Ta kware a fannin Tattalin Arziki kuma ta yi amfani da sana'arta na tsawon shekaru 20 a Masana'antar Banki. Ta zama ‘yar siyasa a shekarar 1999 kuma ta kasance shugabar kwamitin dindindin mai kula da harkokin tattalin arziki, kuɗi da kasafin kuɗi. Ita ce shugabar hukumar gudanarwar bankin Microfinance na Tujane da ke Burundi.[1]


Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 Iranzi, Fabrice (2021-05-01). "Breaking: President Ndayishimiye sacks Burundi Minister of Commerce". RegionWeek (in Turanci). Archived from the original on 2021-05-01. Retrieved 2021-09-27.
  2. "Burundi new President Ndayishimiye breaks Batwa marginalisation jinx as he appoints minister from pygmy tribe". Watchdog Uganda (in Turanci). 2020-06-29. Retrieved 2021-09-27.
  3. AfricaNews (2020-06-29). "Women occupy 30% of Burundi's new cabinet". Africanews (in Turanci). Retrieved 2021-09-27.
  4. Egobiambu, Emmanuel (2 May 2021). "Burundi President Sacks Commerce Minister Amid Fund Embezzlement Claims". Channels TV. Retrieved 17 November 2023.