Ciyawan illiri wata Ciyawa ce mai tsananin kyau musamman ga mai turke/kiwon:-

File:Illiri.jpg

Saniya/sa

Goɗiya/doki

Tunkiya/rago

Akuya/bunsuru

Jaka/jaki.

Duk sukan ci ciyawan illiri, ciyawan illiri ba ya da ƙaiƙaiyi kaman wasu daga cikin ciyayin da Allah ya albarkace mu da su, haka ma ba ya da ƙaya kaman wasu ciyayin, misali kaman su;

Tcaido,

Karangiya,

Ɗonyen raƙuma.

Ciyawan illiri ba ya fitowa sai a lokacin damuna, haka ma ba ya fitowa sai a cikin fadama, a fadamar ma sai wajen da yake da wadataccen sanyi.

Ciyawan illiri yakan girma sosai gwanin sha'awa, haka ma yakan yi ƙonshi ya fitar da kai, yakan yi bunini ya yi ƙwaya kaman kowanne kalan Ciyawa.

Ciyawan illiri yana da gaɓa gaɓa dogaye gwanin sha'awa, yana da tsawon kara da gaɓoɓi, ciyawan illiri a cikin karanta babu toto kaman sauran ciyayi masu nau'in kara kaman; gamba da sauransu. Wannan shi ya bai wa yara damar sukan yi mabusa su na busawa kaman mai busa sarewa.

Roƙonmu ga manoma da gwamnati a samu wata hanya ta rage yin feshi wa ciyayi ko kuma ma a hana sayar da maganin yin feshi ko a fitar da wani tsarin na yanayin ciyawan da za a rukka ma feshi domin gujewa rashin ko ɓatan irin waɗannan kalan ciyayi da Allah ya albarkace mu da su wata rana. Ya kan bushe idan iskan yamma ya buga, masu gini su kan yi amfani da shi a wajen ramno, haka ma akan bai wa dawaki busasshensa a lokacin rani.