Janar Idriss Alkali an haife shi a garin Potiskum, a karamar hukumar Potiskum dake Jihar Yobe a shekarar da Najeriya ta samu 'yan cin kai (wato 1960)[1]

Janar Alkali ya fara karatun sa daga Firamare daga nan ya kara zuwa Sakandire in da bayan ya kammala karatun Sakandiren ya samu gurbin shiga babbar makarantar sojoji na NDA dake Kaduna a shekarar 1980.

Marigayi Janar Idris Alkali yana da matakin karatun shaidar digiri na biyu (Masters degree) wanda yayj a jami'ar tsaro ta kasar Amurka (National Defense University in Washington DC).

Wato yana da digiri na biyu a bangaren ilmin tsaro wanda yayi a makarantar koyon yaki (National War College) dake Amurka, sannan sai wani digiri na biyu a kan tsaro da dabarun yaki a makarantar College of International Security Affairs.

Yana kuma da shaidar wanda ya kammala karatun digiri a bangaren magance ayyukan ta'addanci a duniya (International Counterterrorism) a NDU, sannan yana da digiri akan ilmin yaki (War Studies) wanda yayi a kasar Pakistan (University of Baluchistan, Quetta, Pakistan),

sannan yayi Postgraduate Diploma akan mu'amalar kasashen duniya (Diplomatic Studies) daga jami'ar Westminster dake kasar Burtaniya (University of Westminster, London, UK)

Bayan Janar Idris Alkali ya kammala karatu da karban horo a NDA an karramashi da mukamin mataimakin laftanar (Second lieutenant) a shekarar 1983.

Daga nan aka kaishi ya fara aiki a bangaren sojojin da suka kware a yakin sunkuru (Infantry Corps) amma bai jima ba sai aka kaishi bangaren kwararru masu tattara bayanan sirrin tsaro (Intelligence Corps).

Janar Idriss Alkali yayi ritaya a matsayin babban mai kula da tsare-tsare (Admin) na rundinar sojin Nigeria.

Batan Janar Alkali

gyara sashe

Tun a ranar 3 ga watan Satumban shekarar 2018 aka fara neman Janar Alkali wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja kuma aka daina samun wayarsa a dai dai lokacin da ya isa yankin kudancin Jos cikin motarsa mai lambar Kwara MUN 670 AA, yayinda aka gano motarsa ranar 29 ga watan Satumba a ranar juma’a.

Janar Idris Alkai Ya hadu da ajalinsa a hannun 'yan ta'adda a ranar 3 ga watan Satumba, shekarar 2018 da misalin karfe 12 zuwa karfe 1 na rana, a garin Dura-Du kudancin Jos Jihar Pilato kan hanyarshi na zuwa Bauchi domin ya duba gonarsa kafin ya wuce garinsa Potiskum, sun hallakashi yana da shekaru 58 daidai a duniya watanni 2 bayan yayi ritaya daga aikin soji.[2][3]

Manazarta

gyara sashe