Ibrahim Yaro Yahaya (an haifeshi a ranar 10 ga watan oktoba, shekara ta alif dari tara da arba'in da hudu 1944). Shararren marubucin harshen hausa ne, wanda yayi rubuce-rubuce da yawa a fanninika daban-daban na yaren hausa irin su; adabi, labarun gargagiya, tatsuniyoyi da wasanni nazarin hausa da kasidu masu yawa na harshen hausa.

Ibrahim Yaro Yahaya
Rayuwa
Sana'a
hoton farfesa ibrahim yaro yahaya

Farkon rayuwa da Karatu gyara sashe

An haifi Ibrahim Yaro Yahaya a unguwar 'yandoya ta cikin birnin Kano a ranar 10 ga watan oktoba, shekara ta alif dari tara da arba'in da hudu 1944.

Ya fara Makarantar Allo tun yana yaro. Bai fara karatun zamani ba sai a cikin shekarar alif dari tara da hamsin da takwas 1958,lokacin da aka buɗe makaranta Dantata, ya shiga ajin yamma, ya kammala a cikin 1961. A cikin malamansa na makarantar Dantata akwai Alhaji rufa'i Yahaya da Dr.Kabiru Galadanci da Alhaji Imam Abubakar Wali da Alhaji Umar Faruk Ladan.

 
Wasannin gargajiya na hausawa

Aiki gyara sashe

Yayi koyarwa a makarantar firamare ta dantata daga shekara ta alif dari tara da sittin da daya 1961 zuwa alif dari tara da sittin da biyu 1962. Yasami shiga Kwalejin Horon Malamai ta Bici daga shekarar 1962 zuwa 1966 a inda ya sami takardar shedar malami mai daraja ta biyu. Daga fitowarsa sai yayi [[hedimasta]] a makarantar Horon Akawu-Akawu ta En-En kano wadda aka fi sani da suna Kano N.A Emagency Clerical Training School.

Manazarta gyara sashe