Ibrahim M. Ida

Dan siyasar Najeriya

Ibrahim M. Ida (an haife shi a 15 ga Janairun shekarar 1949) an zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar mazaɓar Katsina ta Tsakiya ta Jihar Katsina, Nijeriya, inda ya fara aiki a ranar 29 ga Mayu shekarata 2007. Shi memba ne na jam`iyyar All Progressives Congress . [1]

Ibrahim M. Ida
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011
Umar Ibrahim Tsauri - Ahmed Sani Stores
District: Katsina Central
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

29 Mayu 2007 - Mayu 2011
District: Katsina Central
Rayuwa
Haihuwa Jihar Katsina, 15 ga Janairu, 1949 (75 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Ida ya sami AIB, London (1977), MSc a harkokin Banki da Tattali, Jami'ar Ibadan a shekarar (1983) da LLB, BL, Jami'ar Abuja (2003). Kafin a zaɓe shi a Majalisar Dattawa ya riƙe muƙamin Kwamishinan Kuɗi, na Jihar Katsina da kuma Sakatare na din-din-din na Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya. Bayan an zabe shi, an naɗa shi kwamitoci kan Dokoki da Kasuwanci, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa mai zaman kanta, Ktudi da Tsaro & Sojoji. [1]

Manazarta gyara sashe