Ibrahim Haruna Abdulkarim wanda aka fi sani da Ibrahim Haruna AK malamin jami'a ne ta Jami'ar Taraya dake Dutsinma. An haifi Ibrahim Haruna AK a watan Nuwamba 28, shekara ta 1988 a garin Katsina dake Arewa Maso yammacin Najeriya.[1]

Ibrahim Haruna AK
 
Ibrahim Haruna AK

Ibrahim Haruna Abdulkarim yayi karatun firamare da sakandare a makarantun Gwamnati dake jihar Katsina. A shekarar 2010 ne ya kammala Hassan Usman Katsina Polytechnic inda ya karanci Business Administration. Bayan ya kammala a shekarar 2011 ya shiga Jami'ar Umaru Musa Yar'adua inda ya karanci Economics. Ya kammala karatun gaba da Degree wato Masters Degree a Jami'ar Taraya dake Dutsinma.

Aiki da Gogewa

gyara sashe

Mal. Ibrahim yayi ayyuka da dama musamman wadanda suka shafi harkar ilimi. Ya fara koyarwa a Makarantar Firamare ta Godiya College Katsina, sannan ya koyar a Makarantar Ilimi ta Amana Community dake cikin Birnin Katsina. Bayan nan kuma yanzu yana koyarwa a Jami'ar Taraya dake Dutsinma.

Manazarta

gyara sashe
  1. https://scholar.google.com/citations?user=9Tdj1BsAAAAJ&hl=en