HUKUNCIN JININ MAI LAUNIN KASA (brownish discharge)

:

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

:

Kafin na fara Al'adata, nakan lura da zubar jini/ruwa mai launin kalar kasa (brown discharge) Kuma Yana kaiwa tsawon kwanaki biyar, Bayan nan kuma sai jinin Al'ada ya biyo. Jinin Al'adar yana daukar tsawon kwanaki takwas bayan kwanaki biyar na farko. Nakan yi Sallah cikin kwanaki biyar ɗin amma sai nake shakkun yin azumi da sallah cikin wa'ennan kwanaki biyar ɗin na farko ko a'a? Don Allah ka bani shawara, Allah ya saka da alkhairi.

:

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

:

Idan cikin kwanaki biyar ɗin da kike ganin ruwa mai launin kasa (brownish discharge) ba haɗe yake da kwanakin da kike ganin jini hailar ki ba, toh ba ya ɗaukar hukuncin jinin Al'ada, don haka zaki yi sallah cikin wa'ennan kwanakin biyar da azumi.

Amma kuma zaki jaddada alwala ga ko wani sallah idan zaki yi. Saboda ya na ɗaukar hukunci ne daidai da na fitsari, amma ba na Al'ada ba.

Kenan haƙan baya nufin cewa bazaki iya yin sallah ba ko azumi, amma zaki rika yin alwala duk sanda kika tashi yin sallah, har sai lokacin da wannan ruwan ya yanke, kamar yadda hukuncin jinin istihaadah (jinin cuta/non-menstrual bleeding) yake ɗauka.

Amma idan wa'ennan kwanaki biyar ɗin haɗe suke (bima'ana babu wani tazaran lokaci a tsakani) da kwanaki takwas da kike yin al'ada, toh hukuncin wannan ruwa mai launin kasa-kasa (brownish discharge) ɗin, daidai yake da na jinin al'ada, don haka bazaki yi sallah ba ko azumi cikin wa'ennan kwanakin.

.

Haka zalika, a karshen Al'adar ki, fitar ruwa mai launin kasa (brownish), ko me fatsi-fatsi (yellowish discharge), baya ɗaukar hukuncin jinin Al'ada, amma ya na zuwa ne karkashin hukuncin istihaadah (jinin cuta), don haka zaki rika yin tsarki ki jaddada alwala akan ko wani sallah idan zaki yi.

Sannan zaki yi sallah da azumi da kuma rayuwar aure da mai gida. Dalili kuwa shi ne hadithin Ummu Atiyyah:

كنا لا نعد الكدرة والصفرة بعد الطهر شيئا " أخرجه البخاري في صحيحه وأبو داود وهذا لفظه).

Ki duba: Majmoo’ Fataawa na Shaykh Ibn Baaz, 10/207

WALLAHU A'ALAM

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ