Hukumar Kula da Ƴan Gudun Hijira, Baƙi, Waɗanda suka rasa muhalli, ta Ƙasa

Hukumar kula da ƴan Gudun Hijira da baƙin haure da ƴan Gudun hijira ta ƙasa ( NCFRMI ), wacce a da aka fi sani da Hukumar ƴan Gudun Hijira ( NCFR ), hukuma ce ta Gwamnatin Tarayyar Najeriya, wacce aka kafa ta a ƙarƙashin doka ta 52 ta shekarar 1989 a yanzu Cap.N21, Dokokin Tarayyar Najeriya, 2004 (NCFRMI Act) don gudanar da al'amuran ƴan gudun hijira, ƴan ci-rani da ƴan gudun hijira a cikin Najeriya.Hukumar na ɗaya daga cikin hukumomi shida da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar kula da jin ƙai da kula da bala’o’i da ci gaban al’umma ta tarayya Najeriya. Babban Kwamishinan tarayya ne yake jagorantar Hukumar.[1][2][3][4]

Hukumar Kula da Ƴan Gudun Hijira, Baƙi, Waɗanda suka rasa muhalli, ta Ƙasa
Bayanai
Iri government agency (en) Fassara

Asali gyara sashe

Gwamnatin tarayyar Najeriya ce ta kafa hukumar kula da ƴan gudun hijira da baƙin haure da ƴan gudun hijira ta ƙasa domin cika ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya mai lamba 319(IV) a ƙarƙashin sashe na 35 na yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya ta 1951.A da dai an san hukumar ne da gudanar da al’amuran ƴan gudun hijira kawai amma daga baya tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya faɗaɗa ta a shekarar 2002.A 2021, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Hon.Imaan Sulaiman-Ibrahim a matsayin kwamishinan tarayya na hukumar.[5]

Jerin Kwamishinan dake wakiltar Hukumar gyara sashe

Tsohon kwamishinan tarayya na hukumar da sabon sun haɗa da:

Manazarta gyara sashe

  1. Quadri, Ope (2019-10-29). "List Of 6 Agencies Under The Ministry Of Humanitarian Affairs, Disaster Management, And Social Development (FMHDS)" (in Turanci). Retrieved 2022-03-30.
  2. "Before Refugees Commission goes from bad to worse". TheCable (in Turanci). 2021-11-25. Retrieved 2022-03-30.
  3. "NCFRMI/UNHCR and Task of managing Refugees in Nigeria". Vanguard News (in Turanci). 2021-02-22. Retrieved 2022-03-30.
  4. "Nigerian govt to provide 350,000 IDPs with start-up skills, capital" (in Turanci). 2020-10-13. Retrieved 2022-03-30.
  5. editor (2022-01-24). "Migration Policy to be Reviewed Soon, Says Commissioner". THISDAYLIVE (in Turanci). Retrieved 2022-03-30.CS1 maint: extra text: authors list (link)
  6. editor (2022-01-24). "Migration Policy to be Reviewed Soon, Says Commissioner". THISDAYLIVE (in Turanci). Retrieved 2022-03-30.CS1 maint: extra text: authors list (link)
  7. "National Commission for Refugees, Migrants and Internally Displaced Persons to Partner with NIMC". National Identity Management Commission (in Turanci). Retrieved 2022-03-30.