Homeward (fim)
Homeward ( Crimean Tatar, Ukraine , Dodomu ) shirin wasan kwaikwayo ne na ƙasar Ukraine, wanda akayi a shekara ta 2019 wanda Nariman Aliev ya bada umurni.[1] An nuna shi a cikin sashin Un Certain Regard a bikin Fim na Cannes na 2019.[2] An zaɓe shi azaman shirin fim na kasar Ukraine a matsayin Mafi kyawun Fim na kasa da kasa a 92nd Academy Awards, amma ba a zaɓe shi ba.[3][4]
Homeward (fim) | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 2019 |
Asalin suna | Evge |
Asalin harshe |
Harshan Ukraniya Crimean Tatar (en) |
Ƙasar asali | Ukraniya |
Characteristics | |
Genre (en) | drama film (en) |
Direction and screenplay | |
Darekta | Nariman Aliev |
Marubin wasannin kwaykwayo |
Nariman Aliev Marysia Nikitiuk |
'yan wasa | |
Tarihi | |
Nominations
| |
External links | |
Specialized websites
|
Labari
gyara sashe'Dan garin Tatar Crimea, Mustafa da dansa Alim sun yi arangama bayan karbar gawar wan su Nazim, wanda ya mutu a sanadiyar yaki tsakanin Rasha da Ukraine.[5] Tarihin rahin jituwar iyalinsu da gwamnati ya tursasa wa Mustafa yin kaura don zuwa aikin hajji don birne dan uwansa a bisa tsarin addinin musulunci ta Crimea. Labarin ya fara ne daga dakin ajiye gawawwaki, sannan a kan hanyar tafiya a cikin wata mota kirar Jeep Cherokee daga Kyiv zuwa gabar tekun Crimean. Bayan rashin barci da bacin rai, motar Jeep din ta lalace a cikin wani rami. Daukar motar zuwa shagon kanikawa mafi kusa, Alim ya hadu da jikar makanikin, wata yarinya 'yar kasar Yukren wacce ta shawo kansa ya tafi kogi. A wannan lokacin ne masu balaguron suka yi asarar lalitarsu ga gungun samarin yankin. Alim da Mustafa sun kara kusantar juna yayin da sukakoyi yadda zsu kare kawunansu kuma su amso lalitarsu. Ciwon Mustafa kuma ya bayyana kuma yana ƙara tsananta lokacin da uba da ɗansu suka isa gidan Uncle Vasya. Gidan bai yi nisa da asalin ƙasar Crimean ba, kuma Mustafa ya shawo kan Kawu Vasya ya ba shi aron kwalekwalen don kammala sauran tafiyarsa.
liyafar
gyara sasheMujallar Collider da jaridar The Guardian sun ayyana shirin a matsayin ayyukan sinimar kasar Ukraine na musamman.[6][7]
'Yan wasan kwaikwayo
gyara sashe- Akhtem Seitablaev a matsayin Mustafa
- Remzi Bilyalov a matsayin Alim
Duba kuma
gyara sashe- Jerin abubuwan da aka gabatar ga lambar yabo ta 92nd Academy Awards don Mafi kyawun Fim na Fasalin Duniya
- Jerin Ukrainian ƙaddamarwa ga Academy Award for Best International Feature Film
Manazarta
gyara sashe- ↑ "The Screenings Guide 2019". 9 May 2019. Retrieved 9 May 2019.
- ↑ "Cannes festival 2019: full list of films". The Guardian. Retrieved 18 April 2019.
- ↑ "Фільм "Додому" офіційно став претендентом на "Оскар" від України". Ukrainian State Film Agency. Retrieved 23 August 2019.
- ↑ "Ukrainian film Homeward about annexed Crimea goes for Oscar". Opinion UA. Archived from the original. on 23 August 2019. Retrieved 23 August 2019.
- ↑ Dalton, Stephen (29 May 2019). "'Homeward' ('Evge'): Film Review". Variety. Retrieved 30 August 2019.
- ↑ Shomer, Jason (12 March 2022). "Best of Ukrainian Cinema, Like 'Homeward' and 'Bitter Harvest'". Collider. Retrieved 11 September 2022.
- ↑ Lodge, Guy (5 March 2022). "Streaming: the best Ukrainian films past and present". the Guardian. Retrieved 11 September 2022.