Helen Wanjiru Gichohi ƙwararriya ce a fannin ilimin halittu ta ƙasar Kenya wacce ita ce shugabar gidauniyar namun daji ta Afirka (AWF) daga shekarun 2007 zuwa shekarata y 2013.

An haifi Helen Gichohi a wata al'ummar harkar noma a tsakiyar Kenya. Ta sami digirin farko na Kimiyya a fannin dabbobi daga Jami'ar Kenyatta sannan ta yi digiri na biyu a fannin Kimiyyar Kiwon Lafiya daga Jami'ar Nairobi. Ta wuce Jami'ar Leicester, inda ta sami digiri na uku a fannin ilimin halittu. Yayin da take aiki don karatun digirinta na uku, Helen ta yi nazarin tasirin ƙonawa da ake sarrafawa akan wuraren kiwo na namun daji a cikin National Park na Nairobi. A Ƙarshe ita ce, ta sarrafa yadda ya kamata, wuta na iya taimakawa wajen kiyaye saɓanin buɗaɗɗen da ke ba da abinci ga namun daji. Ta ce ta shiga cikin ilimin halittu, na wani ɓangare saboda ta fi son yin aiki a waje fiye da a cikin ɗakin gwaje-gwaje. [1]

A cikin shekarar alif dubu da dari tara da casain 1990, yayin da mai bincike a Cibiyar Kare namun daji ta International (WCI), Helen Gichohi ta shirya bayanin tasirin muhalli kan yankin sarrafa fitar da kayayyaki na kasuwanci ga gwamnatin Kenya. Ta zama Darakta na Cibiyar Kare Kayayyakin Afirka (ACC), wanda ke samun goyon bayan ƙungiyar Kare namun daji. A shekarar alif 1998 aka naɗa ta a wani kwamiti mai mutane biyar don ba da shawara ga shugaban Amurka Bill Clinton game da al'amuran muhalli a Afirka. Ta shiga gidauniyar kula da namun daji ta Afirka a watan Fabrairun 2001 a matsayin Darakta na Shirin Zuciya na Afirka kuma a cikin watan Fabrairunshekara 2002 aka naɗa ta mataimakiyar shugabar shirin. A watan Janairun shekara 2006 shugabar ƙasar Kenya ta baiwa Dr. Gichohi lambar yabo ta Great Warrior na Kenya saboda gudunmuwar da ta bayar wajen kiyayewa (conservation).

A cikin shekarar Janairu 2007 kwamitin amintattu ya zaɓe ta a matsayin Shugabar AWF. Ta kuma yi aiki a kwamitin amintattu na Hukumar Kula da namun daji ta Kenya. Helen Gichohi ta fito a matsayin ƙwararriya mai magana a cikin fim ɗin 2009 wanda ya lashe kyautar Milking the Rhino. Tun daga shekarar 2011 ta kasance memba na Kwamitin Ba da Shawara na Gida a Kenya na Kungiyar Kenya Land Conservation Trust. Ta kasance memba na kwamitin amintattu na Kenya Land Conservation Trust Archived 2024-02-23 at the Wayback Machine and of Beads for Education, ƙungiya mai zaman kanta da ke taimaka wa iyaye mata su sami kuɗin tura 'ya'yansu mata zuwa makaranta. Ta kasance mamba ce ta Bankin Equity Kenya, wanda ya fara a matsayin ginin al'umma, daga baya ya zama cibiyar kula da ƙananan kuɗi sannan kuma cikakken bankin kasuwanci.

Littattafai

gyara sashe
  •  Helen Wanjiru Gichohi (1996). The ecology of a truncated ecosystem: the Athi-Kapiti Plains. University of Leicester.
  •  Edmund G. C. Barrow; Helen Gichohi; Mark Infield (2000). Rhetoric or reality?: a review of community conservation policy and practice in East Africa. International Institute for Environment and Development. p. 184.
  •  Jeffrey Worden; Robin Spencer Reid; Helen Gichohi (2003). Land-use impacts on large wildlife and livestock in the swamps of the greater Amboseli ecosystem, Kajiado District, Kenya. LUCID Project, International Livestock Research Institute. p. 100.

Manazarta

gyara sashe
  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Hilpert2010