Hassan Adamu da akafi sani da Hassan sarkin dogarai shine dogari na uku 3 wanda sarkin kano Ado Bayero ya nada, Ya zama Sarkin dogarawan Sarkin Kano a shekara ta alif 1990. Jama'a sun kara sanin sa dalilin wakar da marigayi Mamman Shata ya yi masa mai taken Hassan Sarkin Dogarai

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

An haifi Hassan Adamu sarkin dogarai a shekara ta alif dari tara da ashirin da biyar (1925)

Nadin Sarkin Dogarai

gyara sashe

Hassan Adamu ya kasance Sarkin Dogarai na Uku Da Marigayi Sarkin kano, Mai Martaba Alh Ado Bayero Ya Naɗa a matsayin Shugaban Dogarawan Sarki a Shekarar alif 1990. Kafin Nadin Hassan a Matsayin Sarkin Dogarawan Fadan Kano, Marigayin yana da Wasu Mutane biyu Daban a baya, akwai dan wudil da Adamu, kuma Bayan mutuwar Adamu ne Aka Nada Hassan,Shima bayan mutuwar Hassan a kanada Dan'bala.

Sana'ar Tukin Mota

gyara sashe

Hassan ba Bafade bane, asalin sa direba ne dake Sana'ar tuka mota Kafin daga baya Yazama hadimi ga Galadiman Kani, marigayi Tijjani Hashim, Mutumin daya fara nadashi a matsayin Shamakinsa,Kuma yazama sanadiyyar Shigar sa Cikin fadar Kano.[1]

A shekarar 1990 ne, Bayan mutuwar Sarkin Dogarai dan-wudil, Marigayi galadiman Kano, Tijjani Hashim, yaroki Sarkin Kano Mai martaba Ado Bayero Alfarma yanada Hassan a matsayin Sarkin Dogarai, Saboda tsananin biyayyarsa da kuma jarumtarsa, Sannan ga Soyayya da yake nunawa ga Sarkin. Sarkin dogarai kafin Rasuwarsa yana zaune tare da Iyalansa a unguwar sagagi kusa da Gidan mahaifiyar Sarki Ado Bayero.Kafin daga bisani ya koma Gidan Sarkin Dogarai dake unguwar Dogarai, dake kusada gidan Sarkin Kano. Hassan yayi shura a chikin Sarakunan Dogaran Kano saboda karfi da Jarumta Da kuma tsananin Biyayyansa ga Sarki Ado.[2] Hassan tsayayyan mutum ne, Saboda girma da tsayi har kirari akeyi masa da bishiya.

Hassan ya rasu a shekarar 2007. Yanzu haka Iyalan Hassan sun koma unguwan sagagi asalin gidan mahaifinsu Suncigaba da rayuwarsu bayan Rasuwar sa.

Manazarta

gyara sashe