Harin Bam a Gombe, Yuli 2015
A ranakun 16 da 22 ga watan Yulin a shekara ta 2015, an kai harin bam a birnin Gombe na Najeriya - ga dukkan alamu ƙungiyar Boko Haram mai da'awar jihadi ce ta kai harin. [1] [2]
Harin bam a Gombe, 2015 | ||||
---|---|---|---|---|
attempted murder (en) | ||||
Bayanai | ||||
Kwanan wata | 2015 | |||
Wuri | ||||
|
Wai-wa-ye
gyara sasheRikicin Boko Haram ya tsananta a tsakkiyar shekarar 2010, ciki har da hare-hare a garin Gombe dake arewa maso gabashin Najeriya a watan Disamba 2014, Janairu 2015 da Fabrairu 2015.
Hari
gyara sasheA ranar 16 ga watan Yunin 2015 a Gombe, an kai harin bam sau biyu a wata kasuwa mai cike da cunkoson jama'a da yammacin rana, inda mutane 49 suka mutu, wasu 71 kuma suka jikkata. [1] Bam na farko ya tashi ne a wajen wani shagon sayar da takalma, na biyu kuma ya tashi a wajen wani shagon ɗan China da ke gabansa. [1]
Wani harin
gyara sasheA ranar 22 ga watan Yunin 2015 a Gombe aƙalla bama-bamai biyu sun tashi a tashoshin mota guda biyu, inda suka kashe aƙalla mutane 29. [2]