Hadarin Canjin Yanayi gyara sashe

Duniyarmu idan ka kalle ta a dunkule yadda take, tamkar halitta guda ce domin Allah ya tsara ta yadda ta ke da tsarin daidaita kanta da kanta, yadda za ta ci gaba da kasancewa mattattara ta halittu masu rai da marasa rai. Wannan tsari na daidaiton duniya ya kan sami nakasau idan wani abu ya yi

yawa fiye da yadda ya kamata wanda a sakamakon haka sai ya yi illa ko kawo canji ga sauran tsarin. Tun sanda aka samar da duniya sama da shekaru biliyan hudu da rabi da su ka gabata, tamkar jariri da aka Haifa, haka duniya ta rika habaka sannu a hankali wato daga wani dunkule na wuta har

ta huce ta zama kasa sannan ruwa ya samu wanda daga cikinsa kuma Allah ya samar da halittu masu rai. Tun sanda rayuwa ta fara a doron kasa, an sami halittu iri-iri wadanda su ka iya zama su rayu a sassan duniya daban-daban, kama daga doron kasa, karkashin ruwa da cikin iska da ke sararin duniya har ma da can karkashin kasa inda ya ke da tsananin zafi.

Tarihi gyara sashe

A dogon tarihin duniya an sami canjin yanayi daga zafi mai yawa zuwa ga sanyi mai tsanani, wanda ke samuwa sakamakon abubuwa da dama. Cikin manyan abubuwan da ke kawo canjin yanayi a duniya shine yanayin sanyi ko zafi wanda shi kuma ke samuwa sakamon yadda duniya ke juyawa da zagaya rana, sannan akwai yanayi yadda farantai da ke dauke da nahiyoyin duniya ke motsawa, da kuma shi kansa maganadisun duniya da ke da karfi a dorayen duniya na kudu da arewa. Wadannan abubuwa kan sa dumin duniya ya karu ko ya yi kasa, yayin da ya yi kasa sosai shine ake samun yanayin hunturu mai tsanani a duniya sakamakon kankara da ke mamaye yawancin sassa na duniya. Ko a lokacin ruwan dufana a zamanin Annabi Nuhu irin abinda ya faru kenan sakamakon ruwa ya mamaye duniya sai duminta ya yi kasa sosai yadda wurare da dama su ka daskare su ka zama kankara. A tsawon tarihin duniya an sami yanayi irin wannan sau biyar tun kafin ma zuwan Dan Adam. Wannan canzawar yanayi daga zafi zuwa sanyi, duniya da kanta ke kula da tsarin wajen daidaita shi.

Hasashe gyara sashe

Yanayin sanyi da zai zo nan gaba sabanin wanda aka saba gani ne a baya, saboda zai samu ne sakamakon yadda Dan Adam ke amfani da wannan gida da Allah ya bashi, ta hanyar dumamar yanayi wanda ayyukanmu ke haifar da shi.

Kariya gyara sashe

Allah ya tsara duniya yadda akwai wata rumfa da ke kare mu daga zaruruwan hasken rana masu illa wadanda ba domin wannan rumfa ba, rayuwa a doron kasa za ta yi wahala.

Wannan rumfa, da iska Allah ya samar mana da ita sakamakon kwayar zarra ta halittar iskar odygen da ke sararin sama wadda idan zaruruwan hasken rana masu illa suka doke ta sai ta canza, sakamakon dahuwa, ta koma wata samfurin iskar wadda ake kira ozone. Ita ozone maimakon zaruruwan haske su dafa ta kamar odygen, sai ta zama kamar wani bango na madubi wanda idan sun dake ta sai su yi tsalle baya su koma sama’u maimakon ratso rumfar su iso doron duniya. Wannan iska ta ozone ta yi cincirindo a kimanin kilomita 20-25 idan ka yi can sama, kuma fadinta ya kai kimanin kilomita 60. Don haka wannan rumfa ta ozone ita ke kare halittu daga gurbatattun abubuwa masu guba da za su iya hallaka halittu a doron kasa. Sakamakon kulafucin dan Adam na tarawa da more abin duniya ta hanyar masana’antu da kone-konen dazuka da sauran hanyoyi na gurbata muhalli, shi ke samar da kwayar iskar Co2 waddaidan ta tashi sama ta cakudu da kwayar iskar ozone sai ta sake maida ta kwayar odygen wadda bata iya bada waccan kariya. A yanzu haka an gano cewa hujewar wannan rumfa a sashen doron duniya na arewa, sakamakon irin wadancan ayyuka, ya kai fadin murabba’in kilomita miliyan 20.7 (wato misalin fadin kasar Nigeria sau ashirin da daya kenan).[1]

==Wasu matsalolin==.

Masana'antu gyara sashe

Wannan kariya ta samo asali tun daga lokacin da Dan Adam ya gano kirkirar masana’antu kusan shekaru 300 da su ka gabata a turai, kuma a tsawon wannan lokaci dumamar duniya ya karu da kimanin digiri 3 a ma’aunin zafi kuma ya na karuwa sannu a hankali. Wata babbar illar kuma ita ce ta sare dazuka a fadin duniya domin samar da itace ko katako da filayen noma ko aikin tituna da gidaje. Ana kiyasin cewa a duk minta daya ana sare itatuwa daidai da fadin filin kwallon ball a kowanne minti guda a fadin duniya, kuma ba tare da sake dasa wasu itatuwan ba. Wutar daji, wadda yawanci manoma ke haifarwa wajen share filayen gonaki na daya daga cikin abinda ke haifar da karuwar hujewar wannan rumfa da ta zamar mana garkuwa.

  • A yanzu mun fara ganin illar abubuwan sakamakon wayar gari yananyi na ta canzawa da haifar da fari a kasashen afirka, ambaliyar ruwa a kowanne sashe na duniya, wutar daji musamman wadda ba’a taba ganin irinta ba a bana a can kasar Australiya wadda ta lakume halittu kusan biliyan daya da miliyoyin filayen daji. Sannan mu na gani yadda kankara ke ta narkewa a doron duniya na Arewa (Arctic) da na kudu (Antarctica).
  • Kuma narkewar wannan kankara na kara yawan ruwa a tekunan duniya yadda ambaliya ta ke ta karuwa musamman a garuruwan da ke gabar teku. A nan gaba idan wannan narkewa ta kankara ta ci gaba a yadda take faruwa yanzu saboda dumamar yanayi, garuruwa da ke bakin gabar teku irinsu Lagos nan da yan shekaru kadan ruwa zai mamaye su. Ruwan sha da ake samu daga rafuka da koramu sai ja baya ya ke yi yadda ya fara zama gwal a sassa da dama na duniya kuma masana su na hasashen cewa nan da yan shekaru masu zuwa yadda ake yake-yake a yanzu a kan man fetur haka za’a koma yakoki a kan ruwan sha.


  • Kuma mun ga yadda a yanzu ake tada jijiyar wuya tsakanin kasahe irinsu Egypt da Ethiopia game da ikon tare ruwan kogin Nilu da Kasahen Turkiya, Syria da Irak akan koguna Eupharates da Tigris, Afghanistan da Iran kan Kogin Helmand, Turkiya da Armenia, a kasashen Yemen, China, India, Somalia da Bolivia har mu nan a Nigeriya an fara kai ruwa rana da Nijar kan kogin Kwara.

Ma`adinai gyara sashe

Halayyar dan Adam ta hadama wajen kwakulo ma’adinai daga karkashin kasa irinsu man fetur, kwal, sumunti, kuza da sauransu hakika ya shake wannan duniya tamu tare da wargaza tsarinta na daidaito, abinda idan ba mu gyara ba shi zai jawo hallakarmu gaba daya.

Hakika ba zamu iya kaucewa bukatunmu na yau da kullum ba, gami da hayayyafarmu amma dai za mu iya canza yadda mu ke biyan wadannan bukatu ta hanyar bin hanyoyi da zai ci gaba da baiwa duniya damar ci gaba da tsarinta na daidaito. Za mu iya yin haka ta hanyoyin yin amfani da hasken rana da iska da ruwa wajen samar da hasken lantarkin da mu ke bukata da kuma makamashi na masana’antu da ababen hawanmu.

Kalubale da mafita gyara sashe

Babbar matsalar canjin yanayi shine kasashe matalauta irinsu Nigeriya su ne za su fi dandanawa wajen jin radadin, maimakon manyan kasashe irinsu Amurka da Turai da Chana wadanda su ne ja-gaba wajen kawo gurbacewar yanayi. Wajibi gwamnatoci da mutane su tashi tsaye domin ganin mun canza yadda muke abubuwa a kokarin rage dumamar yanayi da ke ta’azzara canjin yanayi. A Najeriya wajibi ne mu fara tunanin yadda za mu yi wajen tarar wannan annoba da wuri, kafin ta cimmana.

Hanya mafi sauki shine mu fara saka kudade wajen samar da lantarki da makamashi ta hanyar hasken rana wanda Allah ya bamu da kuma iska. Sannan dole jihohin arewa su hadu waje guda wajen ganin sun gina bangon-bishiyoyi wanda tun 1999 karkashin Obasanjo aka fara maganar har aka kafa kwamiti karkashin Atiku Abubuakar domin aiwatar da aikin amma zancen ya bi ruwa.

Idan aka gina bangon bishiyoyi daga Maiduguri zuwa Sokkwato hakika kwararar Hamada za ta tsaya ciki. Sarakunan mu dole su shigo cikin wannan lamari kamar yadda sarakanmu a baya su ka zama jagorori wajen dashen bishiyoyi.

Kwararar Hamada an kiyasta yana kwaranyar tsawon kilomita guda duk shekara, wanda idan ba’a yake shi ba wallahi za’a wayi gari Hamada ta kai teku. A sakawa yaran makaranta cikin sharuddan karbar shaidar kammala karatunsu su dasa bishiya kamar yadda wata kasar gabashin Afirka ta saka. A zamanin tsohon gwamnan Kano Audu Bako ya kirkiri yin irin wannan bango na bishiyoyi a yankin Kazaure da Danbatta abinda ya taimaki yankin wajen yakar Hamada kuma yanzu idan ka shiga wajen zaka tarar ya zama daji. Da ace tun wancan lokaci sauran sassan arewa sun kwaikwayi Audu Bako da yanzu an samar da wannan kariya ga arewacin kasar nan.

Wajibi mu farfado da wannan tsari. Maganin dumamar duniya da samuwar canjin yanayi sune canza yadda muke rayuwa tare da juya akalarmu zuwa ga makamashi mai tsafta wanda za’a iya jujjuya shi: irinsu rana, iska da ruwa. Sannan dole a yaki sare bishiyoyi ta hanyar dasa sabbi.

Tallafi gyara sashe

Kasashen Turai sun ware asusu na Euro miliyan dari domin taimakawa kasashe irin su Nijeriya wajen yaki da canjin yanayi, don haka wajibi daidaikunmu da gwamnatocinmu mu tashi tsaye wajen ganin cewa ko da gangamin dashen bishiyoyi mun fito da shi wanda zai bamu damar samun wadancan kudaden tallafi domin yakar annobar da ke gabanmu.

Idan yanayin sanyi gama duniya (Ice Age) ya dawo da wuri, yadda wasu masana ke hasashe, mu sani cewa turawa da kasashen da su ka ci gaba za su iya jurewa su rayu, amma wallahi mu macewa zamu yi gaba dayanmu saboda ba mu da karfin tattalin arziki ko tsari da za mu iya tunkararsa.


Canjin yanayi na haifar da kwararowar Hamada gyara sashe

kwararowar hamada Wani masanin tsirrai da aikin noma ya bayyana canjin yanayi da cewa daya ne daga abubuwan da ke haifar da kwararowar hamada da fari musamman a kasashe masu zafi.

  • Kamaludden Tijjani Aliyu na cibiyar Samar da amfanin gona na kasashe masu zafi wato IITA ne ya bayyana hakan a yayin zantawa da Freedom Radio a wani bangare na ranar yaki da kwararowar hamada da annobar fari ta duniya da ake gudanarwa a yau. Ya ce, kaso 24 na kwararowar hamada da fari na samo asali da yadda manoma ke yin huda a yayin ayyukan noma, Wanda hakan ke ragewa kasa tasiri.
  • Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso yace, gwamnati zata fara kaddamar da hukuncin doka ga masu sare bishiyu da zarar ta samu sahalewa daga majalisar dokokin jihar Kano.[2]

Manazarta gyara sashe

  1. https://hausa.leadership.ng/hadarin-canjin-yanayi/amp/
  2. https://freedomradionig.com/canjin-yanayi-na-haifar-da-kwararowar-hamada-masani/