Gwanki
Gwanki, Wani kauye ne dake Arewa Maso Yammacin jihar Kano. Garin na Gwanki yana a Karamar Hukumar Bagwai ta jihar Kano, wanda ke ƙarƙashin dagacin garin Gogori. Gwanki ta rabu har zuwa masu unguwanni uku. Unguwa ta farko ita ce Gwanki Babba, ta biyu Gwankin katoge, sai kuma kashi na uku wato Gwankin Dan Kwari sannan akarkashi kowace Gwanki akwai wasu kamar Gwanki babba akwai Gwankin makera da Kuma Gwanki unguwar Dole,da unguwar kwal,Sai gwankin katoge akarkashita akwai gwanki yaro akwai gwankin kufai dl, sai gwankin dankwari akarkashi ta akwai gwankin baban Mero dakuma wani yanki a cikin garin umbawa Wanda ƙarƙashin Gwanki Dan kwari yake wato. Ƙauye Gwanki na da al'umma masu yawa kuma masu son zaman lafiya da juna.[1]
Gwanki | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | jihar Kano |
Yanayi a kauyen Gwanki
gyara sasheKamar ko'ina a Arewacin jihar Kano, kauyen Gwanki na da yanayi mai kyau na noma da kiwo, hakan ne ma ya sa ga baki dayan mutanen garin ba su da sana'a da tafi noma da kiwo.
Yanayin muhalli
gyara sasheYanayin geographical co'ordination na kauyen Gwanki kamar haka, latitude, 11:35degreeN, da kuma Yanayin longtitude na 8,0333degreeE.
Kauyukan da suka zagaye kauyen Gwanki
gyara sashe- Gogori
- Kodon Hayi
- Kodon Kandas
- Sare-sare
- Umbawa
- Dan Isa
- Walawa
- Rigar Are
- Yakanawa
Al'ummar ƙauyen Gwanki Hausawa ne da Fulani, kuma addinin su shi ne musulunci. Kamar dai sauran garuruwan Jihar Kano.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Garba, Abubakar (2002). State, City and Society: Processes of Urbanisation (in Turanci). Centre for Trans-Sahara[n] Studies.