Godwin Emefiele

Masanin tattalin arziki ne Kuma Dan siyasa a Najeriya an haife shi a 1961

Godwin Emefiele, ma'aikacin banki ne a Najeriya wanda ya riƙe muƙamin gwamnan Babban Bankin Najeriya tun ranar 4 ga watan Yunin 2014, har zuwa ranar 9 ga watan Yuni, 2023. Wanda bayan hawan sabon shugaban Nigeria Bola Ahmed Tinubu yadakatar da shi saboda ƙorafi da zarge-zargen almundahana da laifin daya shafi tsaron ƙasa. An haife shi a ranar 4 ga watan Agusta shekarar ta alif ɗari tara da sittin da ɗaya 1961, A jihar Legas ta Najeriya. Emefiele ɗan asalin Ika South ne, yankin Agbor na Jihar Delta.[1][2][3]

Godwin Emefiele
Governor of the Central Bank of Nigeria (en) Fassara

3 ga Yuni, 2014 - 9 ga Yuni, 2023
Sarah Alade
Rayuwa
Haihuwa Agbor, 4 ga Augusta, 1961 (62 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Najeriya, Nsukka
Sana'a
Sana'a Ma'aikacin banki
godwinemefiele.com
Treasury's meeting with Nigerian President Muhammadu Buhari

Ilimi gyara sashe

Emefiele ya halarci makarantar firamare ta Ansar Udin da Maryland Comprehensive Secondary duk a Jihar Legas, kafin ya wuce babbar Jami’ar Najeriya Nsukka (UNN) don yin karatunsa na uku. Ya samu digirin farko a fannin banki da hada-hadar kuɗi, inda ya kammala a matsayin ɗaya daga cikin manyan ɗaliban ajinsa, a shekarar alif ɗari tara da tamanin da huɗu, 1984. Jim kaɗan bayan hidimar matasa ta ƙasa, Godwin Emefiele ya koma UNN don samun digiri na biyu a fannin kuɗi, wanda ya samu a shekarar alif ɗari tara da tamanin da shida, (1986). Hakanan tsohon ɗalibi ne na Ilimin zartarwa a Jami'ar Stanford, Jami'ar Harvard (2004) da Makarantar Kasuwancin Wharton (2005). Jami’ar Nsukka ta Najeriya (UNN) ta ba Gwamnan Babban Banki, Mista Godwin Emefiele digirin girmamawa a fannin harkokin kasuwanci.[4]

Sana'a a kamfanoni masu zaman kansu gyara sashe

A farkon aikinsa, Emefiele ya karantar da harkokin kuɗi da inshora a Jami'ar Najeriya Nsukka, da Jami'ar Fatakwal, bi-da-bi. Ya kuma ɗan yi aiki da vodafone.

Kafin ya koma babban bankin ƙasa, Emefiele ya samu gogewar aikin banki sama da shekaru goma sha takwas. Ya yi aiki a matsayin babban jami’in gudanarwa kuma darakta mai gudanarwa na bankin Zenith Plc. Emefiele ya kasance mataimakin manajan darakta na bankin Zenith Plc. daga shekarar dubu biyu da ɗaya, 2001. Ya yi aiki a matsayin babban darakta mai kula da hada-hadar banki, (baitulmali), kula da harkokin kuɗi da tsare-tsare na bankin Zenith Plc, kuma ya yi aiki a ƙungiyar gudanarwa tun farkonsa. Emefiele ya yi aiki a matsayin darakta a bankin Zenith Plc da Zenith Bank ( Gambia ) Limited. Emefiele yana aiki a matsayin daraktan ACCION Microfinance Bank Limited.[5]

 

Gwamnan babban bankin kasa gyara sashe

Emefiele ya kasance gwamnan babban bankin Najeriya tun shekarar 2014.[6] A wa'adinsa na farko, ya kula da tsarin shiga tsakani na kuɗin shiga bisa umarnin fadar shugaban ƙasa, inda ya samar da Naira ta Najeriya ta hanyar fitar da biliyoyin daloli a kasuwar canji. Ya kuma ɓullo da tsarin canjin kuɗi da yawa, don ƙoƙarin rufe matsi ga Naira da kuma kaucewa raguwar darajar kima. [7]

A shekarar 2019, Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da wa'adin shekaru biyar kashi na biyu ga Emefiele. [8] Wannan shi ne karo na farko da kowa zai yi wa’adi na biyu tun bayan komawar Najeriya kan turbar dimokuraɗiyya a 1999. [9] Sanata Bukola Saraki ya karanta wasiƙar shugaba Buhari a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu, 2019. An tantance shi a ranar Laraba kuma tabbatarwarsa ta zo ne a ranar Alhamis, 16 ga Mayu, 2019.

Rigima gyara sashe

A wani mataki da ba a taɓa ganin irinsa ba na duk wani shugaban babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya tsunduma cikin siyasa na bangaranci da tsarin dokar babban bankin ƙasar wanda ya tanadi cewa dole ne wanda ke riƙe da muƙamin gwamna ya ci gaba da kasancewa a siyasance da cin gashin kansa a kowane lokaci, domin kiyaye yanayin ɓangaranci.

A watan Mayun 2022, Emefiele ya jawo fushin jama'a lokacin da aka bayyana cewa yana neman ya maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari a zaɓen shugaban ƙasa na 2023. Abin da ya fara kamar jita-jita, lokacin da fastocin yaƙin neman zaɓen shugaban bankin suka mamaye babban birnin tarayya na Abuja ba da jimawa ba sai da gungun wasu da ake zargin manoman shinkafa ne suka sayi fom ɗin shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressive Congress A.P.C na Gwamnan CBN. A cikin jerin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Emefiele ya ƙi amincewa da fom ɗin shugaban ƙasar tare da bayyana cewa ba shi da niyyar tsayawa takara. Sai dai kuma cikin hanzari Emefiele ya shigar da ƙara a babbar kotun tarayya da ke Abuja yana neman kotu ta ba hukumar zaɓe da ofishin babban lauyan gwamnati umarnin kada su hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasa. Kotu ta yi watsi da buƙatar, amma ta gayyaci ƴan wasan biyu da su gabatar da jawabi a hukumance kan dalilin da ya sa ba za a amince da buƙatar Emefiele ba. A yanzu haka Emefiele yana fuskantar Shari'a a Nigeria a kan tuhume-tuhume da zargin almundahana da dukiyar ƙasa da kuma janyo zagon ƙasa ga tsaron Nigeria.

Ƴan Najeriya da ƙungiyoyin farar hula sun shigar da ƙara a gaban kotu inda suka buƙaci a tsige Gwamnan CBN daga mukaminsa saboda saɓa dokar bankin ƙoli.

A ranar 10 ga Yuni, 2023, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta tabbatar da kama Emefiele ta shafinta na Twitter. Rahotanni sun ce an kawo shi ne domin yi masa tambayoyi a wani ɓangare na binciken ofishinsa.[1].

A watan Janairun 2024, wata kotun Abuja ta umurci gwamnatin tarayyar Najeriya ta biya diyyar naira miliyan 100 (€100,000) ga Godwin Emefiele saboda tsare shi ba bisa ka'ida ba.[2].

Sauran ayyukansa gyara sashe

  • Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF), tsohon memba na kwamitin gwamnoni (tun 2018) [10]
  • International Islamic Liquidity Management Corporation (IILM), Memba na Hukumar Gudanarwa (tun 2018) [11]

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe

Godwin Emefiele Official Website Archived 2022-12-26 at the Wayback Machine

Duba kuma gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. "Tinubu suspends Emefiele, orders CBN probe". Punch Newspapers (in Turanci). 2023-06-10. Retrieved 2023-06-10.
  2. Adegboyega, Ayodeji (2023-06-10). "Suspended CBN Governor, Godwin Emefiele, arrested, detained". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-06-12.
  3. https://www.bloomberg.com/profile/person/16322920
  4. "UNN Confers Honorary Degree On Emefiele". Leadership Newspaper (in Turanci). 17 May 2019. Retrieved 7 September 2019.
  5. "Central Bank of Nigeria | Home". www.cbn.gov.ng. Retrieved 28 May 2020.
  6. Camillus Eboh and Chijioke Ohuocha (9 May 2019), Nigeria central bank head nominated for second term Reuters.
  7. Camillus Eboh and Chijioke Ohuocha (May 9, 2019), Nigeria central bank head nominated for second term Reuters.
  8. Camillus Eboh (May 16, 2019), Nigeria's Senate confirms second term for cbank governor Emefiele Reuters.
  9. Camillus Eboh and Chijioke Ohuocha (May 9, 2019), Nigeria central bank head nominated for second term Reuters.
  10. Members International Monetary Fund (IMF).
  11. Governing Board International Islamic Liquidity Management Corporation (IILM).