Gireba gireba abin makwalashe ce, data samo asali daga fulawa, ana sarrafa shi ne daga abubuwan amfanin yau da kullum, akwai fulawa, mangyada, ridi (kantu),suga, da farko za'a fara tankade fulawa a roba mai dan fadi, sai a jika suga, a zuba mangyada kadan, sai a juya shi sosai za'aga yayi wara wara, sai a zuba sugan da aka jika, a kwaba shi sosai kar tayi ruwa kwabin kamar na cincin, sai a dauko ludayi karami na shan kunu sai a zuba ridin a ciki sai a dibo wannan kwabin fulawan a zuba kan ridin a daddanna sai a kifa a kan tiren gashi a gasahi. shi kenan sai ci, kuma ana iya amfani da butter a madadin mangyada.