Gbolabo Awelewa
Gbolabo Awelewa[1] shi ne shugaba a fannin tsaron yanar gizo (Cybersecurity) wanda ke da hannu wajen tsara, gina, da kuma gudanar da ingantattun tsarin tsaro da tsari. A yanzu haka, yana aiki a matsayin Babban Jami'in Magance Matsaloli (CSO) a Cybervergent (wanda a da ake kira Infoprive), kamfanin fasaha wanda ke mayar da hankali kan samar da tsaro ta hanyar tsarin yanar gizo da aka sarrafa ta atomatik. Awelewa yana kan gaba wajen gina makomar “Digital Trust.”[2]
Gbolabo Awelewa | |
---|---|
Sunan yanka | Gbolabo Awelewa |
Haihuwa |
4 December 1980 Lagos |
Dan kasan | Najeriya |
Aiki | Tsaron Kwamfuta |
Shekaran tashe | 2005 - Yanzu |
Organization | Cybervergent |
A tsawon aikinsa, ya rike manyan mukamai na shugabanci daban-daban,[3] wanda ya hada da Babban Jami'in Fasaha (Chief Technology Officer), Babban Jami'in Tsaro na Bayanan Sirri (Chief Information Security Officer), da kuma Masanin Tsaro na Kamfanoni (Enterprise Security Architect) a kamfanonin fasahar kudi (Fintech Unicorns), manyan kamfanoni na duniya, da kuma cibiyoyin kudi.[4]
Awelewa fitaccen masani ne a fannin tsaron yanar gizo kuma an bayyana shi a mujallu da kafofin watsa labarai daban-daban.[5] Yana yawan halartar tarurruka da tarukan masana’antu da yawa. Awelewa yana da sha’awa wajen taimaka wa kungiyoyi wajen gina ingantattun tsarin tsaro. Ya sadaukar da kansa wajen ilmantar da mutane da kuma karfafa su don su zama masu wayewa game da tsaron yanar gizo.[6]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "TECHnically: Gbolabo Awelewa says the key to keeping safe from cyber attacks is to always double-check » YNaija". YNaija. 21 December 2016.
- ↑ Onwuegbuchi, Chike (6 May 2024). "Cybervergent's Q1 2024 Report Reveals Rising Threat of Remcos RAT Malware in Financial Sector". Retrieved 26 August 2024.
- ↑ "Cybervegent Harps On Infrastructural, Human Capacities In Cybersecurity To Improve Digital Development – Independent Newspaper Nigeria". 16 November 2023. Retrieved 26 August 2024.
- ↑ Partner, Uma Edwin for (31 October 2023). "Infoprive rebrands as Cybervergent, poised to revolutionise Africa's tech sector with automated cybersecurity solutions". TechCabal. Retrieved 26 August 2024.
- ↑ Omotayo, Boluwatife (6 May 2024). "'Financial sector records spike in malware attacks'". Businessday NG.
- ↑ Michael, Chinwe (9 November 2022). "Rising cybersecurity poses threat to organisation's growth - PwC". Businessday NG. Retrieved 26 August 2024.