Five Roads to Freedom: From Apartheid to the World Cup
Hanyoyi biyar zuwa 'yanci: Daga wariyar launin fata zuwa gasar cin kofin duniya fim ne na shekara ta 2010, wanda Robin Benger da Jane Thandi Lipman suka jagoranta/bada Umarni shirin na duba ga sauyin juyin juya halin Afirka ta Kudu daga maza da mata biyar da suka rayu a ƙarƙashin inuwar wariyar launin fata.
Five Roads to Freedom: From Apartheid to the World Cup | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 2010 |
Asalin suna | Five Roads to Freedom: From Apartheid to the World Cup |
Ƙasar asali | Afirka ta kudu |
Characteristics | |
Genre (en) | documentary film |
Shirin ya mayar da hankali kan mutane biyar daga ko'ina cikin zamantakewa da siyasa: talakawa mutanen da abubuwan da suka faru wakilci ne na gagarumin canje-canje na shekaru 15, da suka gabata, da kuma waɗanda rayuwarsu a cikin 2010.
Hanyoyi biyar zuwa 'Yanci wani shiri ne mai zurfi ga mai shirya fim Robin Benger. A matsayinsa na shugaban ɗaliban Afirka ta Kudu a ƙarshen shekarun 1960, da farkon 1970, an kama shi sau uku saboda ayyukan yaki da wariyar launin fata, kuma daga ƙarshe an kore shi daga ƙasar. Ian Ayres, Robin Benger, Eric Ellena, Jane Thandi Lipman, Joseph Oesi da Christopher Sumpton ne suka shirya fim ɗin.[1][2]
Manazarta.
gyara sashe- ↑ "Broadcaster Magazine". Archived from the original on 2012-07-20.
- ↑ "Film Screening "Five Roads to Freedom: From Apartheid to the World Cup," March 9". CUNY. 23 February 2015. Archived from the original on 9 June 2021. Retrieved 9 June 2021.