Fatima Ali Modu Sheriff (an haife ta a shekarar 1964), a birnin Maiduguri, Jihar Borno Najeriya.[1]

Kuruciya da Ilimi gyara sashe

An haifi Fatima a shekara ta alif 1964 a gabashin Najeriya Maiduguri, jihar Borno. Ta fara karatun ta na firamare a makarantar Shehu Gabai Primary School, Maiduguri. A tsakanin shekarun alif 1970 zuwa 1980s ta zama daliba a Polytechnic na Maiduguri inda ta yi karatu akan gudanar da kasuwanci (Business management).

Aiki gyara sashe

Fatima Modu tana da matukar tausayi musamman ga mata da kananan yara. Hakan yasa tayi fice ta fuskar tallafin kudi da magunguna ga yara da mata. Ta rike mukamai da dama na ma’aikatu masu zaman kansu. Tana daga cikin kusoshin kungiyoyin mata kamar National Council for Women Societies, Nigerian Association of Women Journalists among others.

Nassi gyara sashe

Kabir, Hajara Muhammad,. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.

Manazarta gyara sashe

  1. Kabir, Hajara Muhammad,. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.