Ellen Johnson Sirleaf

Shugabar Kasar Laberiya ta 24

Ellen Johnson Sirleaf an haife ta ne a ranar 29 ga watan Oktoban 1938 a garin Monrobia ta kasar Liberia wacce ta kasance shugabar kasar Liberia ta 24 a tsakanin 2006 zuwa 2018. Sirleaf ita ce mace ta farko da aka fara zaba a matsayin shugabar kasa a fadin nahiyar Afrika.[1]

Ellen Johnson Sirleaf
24. Shugaban kasar Liberia

16 ga Janairu, 2006 - 22 ga Janairu, 2018
Gyude Bryant - George Weah (en) Fassara
Finance Minister of Liberia (en) Fassara

1979 - ga Afirilu, 1980
Rayuwa
Haihuwa Monrovia, 29 Oktoba 1938 (85 shekaru)
ƙasa Laberiya
Mazauni Washington, D.C.
Nairobi
Monrovia
Harshen uwa Turanci
Ƴan uwa
Abokiyar zama unknown value  (1956 -  1961)
Ƴan uwa
Karatu
Makaranta University of Colorado (en) Fassara
John F. Kennedy School of Government (en) Fassara
Madison Business College (en) Fassara associate degree (en) Fassara : Accounting (en) Fassara
University of Wisconsin–Madison (en) Fassara
College of West Africa (en) Fassara
(1948 - 1955)
Jami'ar Harvard
(1969 - 1971) Master in Public Administration (en) Fassara
University of Colorado Boulder (en) Fassara
(1970 -
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, Mai tattala arziki, entrepreneur (en) Fassara da marubuci
Employers Bankin Duniya
HSBC (en) Fassara
Open Society Initiative for West Africa (en) Fassara
Citibank (en) Fassara  (1981 -  1985)
United Nations Development Programme (en) Fassara  (1992 -  1997)
Kyaututtuka
Mamba Alpha Kappa Alpha (en) Fassara
The Links (en) Fassara
Imani
Addini Methodism (en) Fassara
Jam'iyar siyasa Unity Party (en) Fassara
True Whig Party (en) Fassara
IMDb nm2770344

Karatu gyara sashe

Sirleaf ta yi karatunta ne a College of West Afrika inda ta fara da karantar darasin ilimin lissafi, ta kuma kammala karatun nata ne kasar Amurka, sannan ta kuma yi karatu a Madison Business College da kuma jami’ar Harbard. Ta sake komawa kwalejin CWA inda ta yi digirinta tare da samun Bachelor of Arts a fannin tattalin arziki a cibiyar tattalin arziki ta jami’ar Colorado Boulder, ta kuma halarci jami’ar Harbard, ta yi digirinta na biyu a fannin gudanar da mulki.[2]

Aiki gyara sashe

 
Ellen Johnson Sirleaf

Bayan kammala karatunta ta koma kasarta na Liberia domin yin aiki a gwamnatin William Tolberst a matsayin mataimakiyar ministan kudi daga 1971 zuwa 1974. Daga baya kuma ta yi aiki a yammaci, aikin babban bankin duniya a Caribbean da kuma Latin America. A shekarar 1979, aka nadata mukamin ministan kudi wacce ta yi a shekarar 1980. Daga baya kuma ta yi aiki da Citibank daga baya kuma ta nausa bankin Ekuator. Ta sake komawa kasar Laberiya domin kujerar sanatan Montserrado a 1985, zabe wanda ya wanda ya cika da hatsaniya. Madam Sirleaf dai ta cigaba da kutsa kanta cikin lamarin siyasa. A karin farko a shekarar 1997 ta nemi takarar shugaban kasa amma Charles Taylor ya kada ita.

Shugabanci gyara sashe

 
Ellen Johnson Sirleaf da wata shugaba

A shekarar 2005 ta samu nasarar zama shugaban kasa bayan cin zabe da ta yi, inda ta shiga ofishinta a ranar 16 ga watan Janairun 2016. An sake zabinta shugaban kasar a 2011. Ita ce mace ta farko da aka fara zaba a matsayin shugaban kasa guda a dukanin nahiyar Afrika. Ta samu nasarar lashe kambun Nobel Peace Price a 2011, wanda aka bata bisa himmar da ta nuna wajen daukaka daraja da kimar mata a Afrika da ma duniya. Sannan ta samu lambobin yabo daban-daban bisa kwazonta bisa kyautata shugabanci na kwarai.[3] A watan Yunin 2016 aka zabi Sirleaf a matsayin shugabar ECOWAS, wacce ta sake zama mace ta farko da ta fara shugabanta wannan babbar kungiyar tun da aka kafata. Ta auri mijinta James Sirleaf wanda ya taimaka mata wajen cimma nasarori daban-daban, sun kuma haifi ‘ya’ya hudu a tare. A shekarar 1992, Sirleaf ta kasance daraktan shirin majalisar dinkin duniya, wacce jami’ar da ke kula da shiyya guda tare da zama mai taimaka wa babban sakataren majalisar dinkin duniya. A lokacin da take aiki da UN, taan daga cikin muhimman mutane bakwai da aka fitar a 1999 da aka daura musu alhakin bincikar kisan mummuken Rwanda.[4]

Lambobin Yabo gyara sashe

 
Ellen Johnson Sirleaf

Lambobin yabon da ta samu a rayuwarta suna da matukar yawa, ta kuma zama kallabi a tsakanin rayuwa.[5]

Manazarta gyara sashe